Magidanci Ya Koma Yi Wa Matarsa Kallon Yar Uwarsa, Yana Duba Yiwuwar Sakinta

Magidanci Ya Koma Yi Wa Matarsa Kallon Yar Uwarsa, Yana Duba Yiwuwar Sakinta

  • Wani magidanci ɗan Najeriya koka cewa ya dai na son matarsa wanda a dalilin hakan yana duba yiwuwar rabuwa da ita
  • Tsawon shekara biyu da suka wuce magidancin ya ci gaba da haƙuri da ita duk da cewa son da yake mata ya fice, inda ya koma yana mata kallon ƴar uwa
  • Matsalar da yake fuskanta shi ne baya son ya sake ta ya tarwatsa kan iyalansa, sannan baya da matsala wajen ɗaukar dawainiyarta fannin kuɗi

DUBA NAN: Bibiyi shafin Legit.ng Hausa a kafar TikTok. Kada ka bari bidiyo mai daukar hankali ya wuce ka!

Wani magidanci ɗan Najeriya yana duba yiwuwar rabuwa da matarsa saboda ya dai na jin son ta, gaba ɗaya a zuciyarsa.

A cewar magidancin, sama da shekara biyu da suka wuce ya dai na sonta sannan baya tunanin zai iya ƙara wata ɗaya yana zaune da ita a matsayin matarsa.

Magidanci na duba yiwuwar rabuwa da matarsa
Magidancin ya ce son matarsa ya fice a zuciyarsa Hoto: Lighthouse Films, Hill Street Studios
Asali: Getty Images

Wani sananne a Twitter mai suna Sir Dickson, shi ne ya sanya bayanin magidancin, inda ya yi masa nuni da cewa ba komai ba ne kuɗi su ke magani sannan ya ba shi shawara ya tsaya ya daidaita gidansa maimakon ya saki matarsa.

Kara karanta wannan

Kyakkyawan Kurma Ya Koka Kan Rashin Samun Budurwa, Ya Ce 'Yan Mata Sun Ki Yarda Su Yi Soyayya Da Shi

Magidancin ya bayyana cewa ba ya da wata matsala wajen ɗaukar ɗawainiyar matarsa ta fannin kuɗi, inda ya ƙara da cewa yana da su sosai.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Magidancin ya koka cewa ba zai iya ƙara wata ɗaya yana zaune tare da ita ba, inda ya ce dole sai ya sake ta. Damuwarsa guda kawai ita ce rabuwarsu ka iya tarwatsa masa iyali.

Ƴan soshiyal midiya sun yi bayyana ra'ayoyinsu kan labarin magidancin

@queenchellan ta rubuta:

"Lmao!! babu inda za ka, ƙarya kake!! Amma a aje wasa gefe! Ka je wajen masu bayar da shawara kan aure tare da matarka. Ka yi kyakkyawar niyyar neman gyara tsakaninku. Ka yi ƙoƙarin gyara aurenka maimakon ka ce ka haƙura. Aure aiki ne tuƙuru ba na ragwayen mutane ba ne."

@ckkllyn ya rubuta:

"Wannan shi ne dalilin da ya sanya na ce aure ba soyayya ba ne kadai saboda dole ne ka tabbatar cewa idan ka shiga ka shiga kenan babu wani batun son ya gudu. Aure ba wai alaƙar saurayi da budurwa ba ne wacce da ka ji ba daidai ba za ka ce ka fasa."

Kara karanta wannan

APC: Adamu Ya Yi Murabus Ne Bayan Ya Gano Kotu Ta Rushe Zaben Tinubu? Gaskiya Ta Bayyana

Matar Aure Ta Koka Bayan Mijinta Ya Kara Aure

A wani labarin kuma, wata matar aure ta koka bayan mijinta ya yi mata abokiyar xama ba tare da saninta ba.

Matar auren wacce take zaune a ƙasar Amurka tare da mijinta, ta bayyana cewa mijin na ta ya lallaɓo Afirika ya ƙara wani auren ba tare da ta sani ba.

Asali: Legit.ng

Online view pixel