Abubuwa 4 Da Ya Kamata Ku Sani Game Da Mutumin Da Ya Kashe Sama Da Miliyan 10.7 Don Ya Zama Kare

Abubuwa 4 Da Ya Kamata Ku Sani Game Da Mutumin Da Ya Kashe Sama Da Miliyan 10.7 Don Ya Zama Kare

  • Ya dauki wani mutumin kasar Japan mai suna Toco tsawon kwanaki 40 da kudi sama da naira miliyan 10 kafin ya cimma burinsa na son zama wani dabba
  • Dan kasar Japan din, wanda ya fito cikin kayan kare, ya ce ya damu kuma yana ta tsoron fitowa a bainar jama'a
  • Legit.ng ta jero wasu abubuwa hudu masu ban sha'awa game da mutumin da ya yadu bayan ya cimma mafarkinsa na son zama kare

Wani mutumin kasar Japan, mai suna Toco ya yi suna sosai a yanar gizo bayan fitowarsa a karon farko a matsayin mutumin kare.

Toco, wanda ya samu tarin mabiya a YouTube da TikTok, ya biya wani kamfani mai suna Zeppet zunzurutun kudi har naira miliyan 10.7 domin dinka masa kayan kare.

Ya cimma burinsa na son zama kare
Abubuwa 4 Da Ya Kamata Ku Sani Game Da Mutumin Da Ya Kashe Sama Da Miliyan 10.7 Don Ya Zama Kare Hoto: New York Post
Asali: UGC

Legit.ng ta jero wasu abubuwa hudu masu ban sha'awa game da Toco, mutumin kare da zai tsuma zukata.

Kara karanta wannan

“Ya Kashe Miliyan 10.7”: Wani Mutum Ya Mayar Da Kansa Kare, Ya Fito Bainar Jama’a Cikin Shigarsa

1. A cewar MailOne, Toco ya ce mafarkinsa ne tun yana dan karamin yaro ya zama wani dabba kuma sai da ya jira tsawon kwanaki 40 don Zeppet ya dinka masa rigar.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

2. New York Post ta rahoto cewa Toco ya zabi zama kare ne saboda abun da ya bayyana a matsayin rashin bambanci mai girma tsakanin jinsin da mutane.

3. Duk da tarin mabiyansa a fadin kafofin sada zumunta, har yanzu mutumin kasar Japan din bai bayyanawa duniya wanene shi ba kuma ya boyewa makusanta da yan uwansa.

4. Yayin da mutane da dama ke tunanin kawai wani buri ne ga Toco son zama kare, mutumin kasar Japan din ya ce hakan abu ne da yake sha'awa.

Toco, mutumin kare ya bayyana

A baya Legit.ng ta rahoto cewa Toco, mutum mai siffar kare ya bayyana a bainar jama'a a karo na farko.

Kara karanta wannan

"Ba Su Mutunta Ni Ba": Wani Mutum Da Ya Rasa Aikinsa Ya Saki Matansa 3 Bayan Sun Ci Amanarsa

A yanzu kafar Toco na Youtube yana da mutane fiye da 47,000 da suke bibiyarsa. A daya daga cikin bidiyon, Toco ya bayyana karara cewa zama tamkar wani kare mafarki ne da ya zama gaskiya. Ya rubuta:

"Sunana Toco, ina so in zama dabba kuma na zama kare. Wannan kafar za ta kawo maku bidiyoyin kare na daban a cikinsu! A wannan lokacin, na samu damar cika mafarkina da na dade ina yinsa tun ina dan karamin yaro; zama kare da yin tattaki a waje!"

Asali: Legit.ng

Online view pixel