Manyan Labarai A Yau
Ƴan bindiga sun sace bayin Allah masu yawa bayan sun ɓadda kama ta hanyar yin shigar mata a jihar Zamfara. Adadin yawan mutanen da suka sace bai bayyana ba.
Gwamnan jihar Neja, Mohammed Umaru Bago ya gana da shugaban hukumar sojojin saman Najeriya kan mummunan harin da ƴan bindiga suka kai wa dakarun sojoji a jihar.
Miyagun ƴan bindiga sun kai wani sabon harin ta'addanci a jihar Plateau, inda suka halaka wasu malaman makaranta har mutum biyu, waɗanda sabbin ma'aurata ne.
Darekta Janar na ƙungiyar yaƙin neman zaɓen Atiku Abubakar ta National Solidarity Movement for Atiku/Ifeanyi Okowa (NSM), Muhammad Dakat, ya rasu ya bar duniya.
Matashiya ta ja hankalin duniya bayan da ta hakura da gadon kudin da za ta samu daga iyayenta don ta auri sahibinta da suka hadu a jami’a, mahaifinta baya so.
Manyan masu rarraba kayan mai masu zaman kansu sun rufe gidajen mansu saboda tsoron yiwuwar kara farashin man fetur. Ana tunanin lita za ta iya kaiwa N1000.
Ana ci gaba da neman wani dan Najeriya da ya bace da wata mota da ta kai Naira miliyan 23 da aka ba shi ajiye. An sa shi wanke motar ne sai baa sake ganinsa ba.
Wata budurwa ƴar Najeriya ta samu kyautar maƙudan kuɗaɗe bayan ta yi wani halin kirki. Budurwar ta cika da farin ciki bayan an gwangwajeta da kyautar kuɗaɗen.
Shugaba Tinubu na Najeriya kuma shugaban Kungiyar Raya Tattalin Arzikin Kasashen Afirka Ta Yamma, ECOWAS, na duba yiwuwar tura sojoji zuwa Jamhuriyar Nijar.
Manyan Labarai A Yau
Samu kari