Gwamnan Jihar Neja Da Shugaban Hukumar Sojojin Saman Najeriya Sun Sanya Labule

Gwamnan Jihar Neja Da Shugaban Hukumar Sojojin Saman Najeriya Sun Sanya Labule

  • Gwamnan jihar Neja, Mohammed Umaru Bago, ya garzaya Abuja domin sanya labule da shugaban hukumar sojojin saman Najeriya
  • Ziyarar ta gwamna Bago na zuwa ne bayan ƴan bindiga sun aikata babban ta'asa kan dakarun sojoji a jihar Neja
  • Bago ya aike da saƙon ta'aziyyarsa na asarar rayukan mazan faman da aka yi inda ya buƙaci sojojin ka da su gaji wajen taimakon jihar

FCT, Abuja - Shugaban hukumar sojojin saman Najeriya, AM Hassan Bala da gwamnan jihar Neja, Mohammed Umaru Bago, sun sanya labule kan jirgin sojin saman da ƴan bindiga suka harbo a jihar.

Aƙalla sojoji 20 ne suka halaka a wani kwanton ɓauna da ƴan bindiga suka yi musu akan titin hanyar, Zungeru-Tegina a jihar Neja a daren ranar Lahadi.

Gwamna Bago ya ziyarci shugaban sojojin sama
Gwamna Bago ya kai ziyarar ne domin jaje kan harin 'yan bindiga Hoto: Dailytrust.com
Asali: UGC

Haka kuma aƙalla sojoji bakwai da ƴan sakai biyar ne suka samu raunikan bindiga inda aka kai su asibitin ƙwararru na IBB da ke a Minna babban birnin jihar.

Kara karanta wannan

Innalillahi: 'Yan Ta'addan Jeji Sun Halaka Sojoji 20 a Wani Hari Na Kwanton Ɓauna a Jihar Arewa

Dalilin ziyarar gwamna Bago

Jaridar Daily Trust ta rahoto cewa, gwamnan wanda ya fara da yin shiru na minti ɗaya saboda waɗanda suka rasa ransu, ya buƙaci sojojin sama da dukkanin dakarun soji da su matsa ƙaimi wajen kakkaɓe ƴan bindiga.

DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka

A kalamansa:

"A yau mun zo nan ne saboda abubuwa guda uku. Na farko, yin ta'aziyya kan rasuwar jami'an ku da wasu sojoji da aka halaka a yankin Wushishi na jihar mu."
"Na biyu, domin nuna godiyar mu. Hukumar sojojin sama ta taimakawa jihar Neja. Roƙon mu shi ne kada ku gaji. Za mu ba ku goyon baya. Muna tare da ku."

A na shi ɓangaren, shugaban hukumar sojojin saman, ya bayyana cewa an ɗauki matakai domin ganin hakan bai sake aukuwa ba a nan gaba. Ya ƙara da cewa indai har jiragen saman za su riƙa gittawa, abin da ya farun ba za a iya cewa ba zai iya sake faruwa ba.

Kara karanta wannan

Jami'an Hukumar Kwastam Sun Kama Harsasai 1,245 Da Aka Boye Cikin Buhunan Shinkafa 'Yar Waje

Jihar Neja Za Ta Samu Filin Jirgin Sama

A wani labarin na daban kuma, kun ji cewa filin tashi da saukar jiragen sama da ake aikin ginawa a jihar Neja na dab da kammaluwa.

Gwamnan jihar Neja, Umaru Bago shi ne ya bayar da wannan tabbacin na cewa tuni hat gwamnatinsa ta fara tattaunawa da kamfanonin jirage masu zaman kansu domin fara jigila a filin jirgin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng