Bayanai Kai Tsaye Kan Juyin Mulkin Nijar: Sojojin Nijar Za Su Gurfanar Da Bazoum Kan Zargin Cin Amanar Kasa

Bayanai Kai Tsaye Kan Juyin Mulkin Nijar: Sojojin Nijar Za Su Gurfanar Da Bazoum Kan Zargin Cin Amanar Kasa

A ranar Laraba, 26 ga watan Yuli, sojoji sun yi juyin mulki a Jamhuriyar Nijar yayin da sojoji masu tsaron shugaban kasa suka tsare Shugaba Mohamed Bazoum.

Kungiyar Raya Tattalin Arzikin Kasashen Afirka Ta Yamma, ECOWAS, karkashin jagorancin Shugaban Bola Tinubu na Najeriya, ta sanar da takunkumi daban-daban ciki har da yiwuwar tura sojoji idan shugabannin sojojin juyin mulki ba su sauka daga mulki ba.

Kasance tare da Legit.ng Hausa domin cigaba da samun bayanai kai tsaye dangane da lamarin.

Jamhuriyar Nijar: Sojoji 6 da wasu da ake zargin mayakan masu ikirarin jihadi sun mutu yayin musayar wuta yayin da ake rikicin Nijar

Wani rahoto da ke fitowa ya tabbatar da kashe sojojin Nijar shida da wasu mutane goma da ake zargin masu ikirarin yaki don jihadi ne a ranar Lahadi, 13 ga watan Agusta.

Hakan na faurwa ne bayan sojoji sun hambarar da Shugaba Mohamed Bazoum na Nijar sun kuma tsare shi.

A cewar shaidun gani da ido, an tattaro cewa mayakan masu ikirarin jihadin sun taho ne kan babura suka yi wa sojojin harin kwantar bauna a Sanam, yammacin kasar.

Legit.ng ta tattaro cewa Sanan wani yanki ne da kasashe uku wato Nijar, Mali da Burkina Faso ke da iyaka, kuma mayakan sun saba kai hari wurin sosai.

An kuma tattaro cewa lamari irin wannan ya faru a yankin a ranar Laraba, 9 ga watan Agusta, na farkonsa bayan Janar Abdourahamane Tchiani ya yi juyin mulki.

Janar Tchiani ya bada hujjar cewa ya yi wa Bazoum Juyin mulki ne saboda tabarbarewar tsaro a Nijar.

Juyin Mulkin Nijar: Zullumi Yayin Da Sojojin Juyin Mulki Ke Shirin Gurfanar Da Tsararren Shugaba Bazoum

Niamey, Nijar - Sojojin da suka yi juyin mulki a Nijar karkashin jagorancin Janar Abdourahamane Tchiani sun bayyana cewa za a gurfanar da hambararren shugaban kasa Mohamed Bazoum kan zargin cin amanar kasa.

Kamar yadda Al-Jazeera ta rahoto, daya cikin shugabannin sojojin Kanal-Manjo Amadou Abdramane ya tabbatar da hakan a daren ranar Lahadi.

Ya ce:

"Kawo yanzu gwamnatin Nijar ta tattara hujoji domin gurfanar da hambararren shugaban kasa da abokan harkallarsa na gida da kasashen waje a kotun kasa da kasa da kasa kan babban cin amanar kasa da yin zagon kasa ga tsaron cikin gida d wajen Nijar."

Juyin Mulkin Nijar: ECOWAS ta umurci sojojinta su daura damarar yakar sojojin da suka hambarar da Bazoum

FCT, Abuja - Kungiyar raya tattalin arzikin kasashen Afirka ta Yamma, ECOWAS, ta umurci dakarunta su dawo da oda ta kundin tsarin mulki a Jamhuriyar Nijar.

Shugaban hukumar ECOWAS, Omar Alieu Touray ne ya bayyana hakan yayin karanto sakon bayan taro da kungiyar ta yi a Abuja a ranar Alhamis.

Taron ECOWAS: Tinubu ya bukaci a cigaba da tattaunawa don warware rikicin Nijar

FCT, Abuja - Shugaban kungiyar ECOWAS, Shugaba Bola Tinubu, ya ce yana da muhimmanci a mayar da hankali kan tattaunawa don warware rikicin Jamhuriyar Nijar.

A cewar shugaban na Najeriya, ya zama dole kungiyar ta cigaba da tuntubar shugabannin sojojin da ke kasar da ke makwabtaka da Najeriya don ganin sun mayar da Shugaba Mohamed Bazoum kan mulki.

Shugabannin yan tawaye sun kafa sabuwar gwamnati a yayin da ECOWAS ke daukan sabbin matakai

Rahotanni da ke fitowa sun tabbatar da cewa shugabannin sojoji a Jamhuriyar Nijar sun kafa sabuwar gwamnati, a cewar wata doka da suka sanar a cikin jawabi da aka fitar kai tsaye a talabijin.

A cewar France 24, Farai Minista Ali Mahaman Lamine Zeine zai jagoranci gwamnati na mutum 21, tare da janar na sojoji daga sabuwar majalisar mulki ta soja da suke jagorantar tsaro da harkokin cikin gida.

Shugabannin Kasashen ECOWAS sun fara taro a Abuja

Kungiyar Bunkasa Tattalin Arzikin Kasashen Afirka ta Yamma, ECOWAS, ta fara taro kan Nijar a birnin tarayyar Najeriya, Abuja.

Shugaba Bola Tinubu na Najeriya, wanda shine shugaban ECOWAS din ya kira wani taron bayan karewar wa'adin kwana bakwai da kungiyar ta bada don mayar da Bazoum kan mulki.

Sojojin na Nijar sun yi biris da wa'adin hakan yasa ECOWAS ta kara wasu takunkumin.

Kungiyar ta yi barazanar daukan matakin soji; lamarin da sassa da dama suka nuna rashin goyon baya musamman a Najeriya.

A halin yanzu ga shugabannin kasashen da suka isa Abuja kamar yadda Daily Trust ta rahoto sune:

1. Julius Maada Bio na Sierra Leone

2. Umaro Mokhtar Sissoco na Guinea Bissau

3. Everiste Ndayishimiye na Burundi

4. Alassane Ouattara na Cote d’Ivoire

5. Mohamed Ould Ghazouani na Mauritinia

6 . Nana Akofo-Ado na Ghana

7. Macky Sall na Senegal

8. Patrice Talon na Benin Republic

Wadanda ake jiran isowarsu

1. Faure Essozimna Gnassingbé Eyadéma na Togo

2 Adama Barrow na The Gambia

Juyin Mulki: Bidiyo ya fito yayin da Sanusi II ya gana da shugaban sojojin Nijar

Khalifan Darikar Tijjaniya, Muhammadu Sanusi II ya gana da Abdourahamane Tchiani, shugaban sojojin da suka karbe mulki a Nijar bayan hambarar da Shugaba Mohamed Bazoum.

Ziyarar da Sanusi ya kai tare da Sarkin Damagaran ba za ta rasa nasaba da neman sulhu tare da yadda za a mayar da mulki hannun farar hula ba.

Kasashen duniya da dama sun yi tir da juyin mulkin tare da kira ga sojojin su gaggauta mika mulki.

Kungiyar ECOWAS ta saka wa Nijar takunkumi daban-daban bayan sojojin sun ki amsa kirar da aka musu na mika mulki ga Bazoum.

Shugaba Bazoum da iyalansa suna cikin mawuyacin hali, sabbin bayanai sun fito

Nijar, Niamey - Shugaban Nijar Mohamed Bazoum da iyalansa suna rayuwa a cikin yanayi mara dadi.

Kamar yadda France 24 ta rahoto, ana tsare da shugaban kasar da iyalansa ba tare da lantarki ba ko abinci.

An tabbatar da hakan a ranar Laraba, 9 ga watan Agusta, cikin wata sanarwa da jam'iyyar siyasar hambararren shugaban da ake tsare da shi ta fitar.

An Tsare Dan Jakadar Nijar a Faransa a Niamey

Nijar, Niamey - Wani rahoto da ke fitowa ya tabbatar da cewa sojojin da suka yi juyin mulki sun tsare Idrissa Kane a Jamhuriyar Nijar a ranar Laraba, 9 ga watan Agusta.

Idrissa Kane da ne ga Aïchatou Boulama Kané, hambarrariyar jakadar Nijar a Faransa wacce ta yi mubaya'a ga hambararre kuma tsararren Shugaba Mohamed Bazoum.

Kamar yadda France 24 ta rahoto, ana zargin Kane na da hannu kan binciken zargin almundaha na kudi da Hukumar Yaki da Rashawa na Nijar, Halcia, ke yi.

Kane a halin yanzu shine shugaban hukumar tura sakkoni na Nijar, a yanzu babu tabbas idan an tsare shi ne saboda zargin rashawa ko kuma biyayya da mahaifiyarsa ke yi wa Shugaba Bazoum da rashin mubiya'a ga sojojin da suka yi juyin mulki.

Juyin Mulkin Nijar: Shugabanin sojoji na ECOWAS sun yi taro a Abuja

FCT, Abuja - Shugabannin rundunar sojoji na Kungiyar Raya Tattalin Arzikin Kasashen Afirka ta Yamma sunyi taron gaggawa a Abuja yayin da sojoji suka karbi mulki a Nijar.

Shugabannin sojojin wadanda suka hadu a hedkwatar tsaro a Abuja a ranar Juma'a, 4 ga watan Agusta suna kira ga wadanda suka yi juyin mulkin su rungumi zaman lafiya kuma su saki tsararren shugaban Nijar, Mohamed Bazoum.

Juyin Mulkin Nijar: Matakin Shugaba Tinubu na neman amincewar Majalisa don tura sojoji

FCT, Abuja - A yayin da sojoji suka karbi mulki a Jamhuriyar Nijar, shugaban kungiyar raya tattalin arzikin kasashen Afirka ta Yamma, ECOWAS, kuma shugaban Najeriya, Bola Ahmed Tinubu, ya dauki matakin neman goyon bayan Majalisar Najeriya domin tura sojoji su kaiwa Janar Abdourahamane Tchiani, wanda ya shirya juyin mulkin hari.

Hakan na zuwa ne bayan juyin mulkin da Janar Tchiani da mukarrabansa suka yi ta yi nasara tare da kama kuma da tsare Shugaba Mohamed Bazoum.

Don haka, ECOWAS ta bada wa'adin kwana bakwai ga Janar Tchiani ya mika mulki ga Shugaba Bazoum ko ya fuskanci takunkumi da harin sojoji.

Online view pixel