Budurwa Ta Hakura da Naira Biliyan 300 da Za Ta Gada Daga Mahaifinta Don Ta Auri Masoyinta

Budurwa Ta Hakura da Naira Biliyan 300 da Za Ta Gada Daga Mahaifinta Don Ta Auri Masoyinta

  • Wata gimbiyar Malaysia Angeline Francis ta hakura da naira biliyan 300 da za ta gada domin ta auri sahibinta da suka hadu a jami'ar Oxford
  • Mahaifinta Khoo Kay Peng, attajirin dan kasuwa, ya sallamawa duniya ita sannan ya nemi ta zaba tsakanin kudi da soyayya
  • Labarinsu ya burge mutane a fadin duniya, domin ya nuna jiga-jigan soyayya, sadaukarwa, da matsin lamba daga al'umma

DUBA NAN: Bibiyi shafin Legit.ng Hausa a kafar TikTok. Kada ka bari bidiyo mai daukar hankali ya wuce ka!

A wani labari da ya ja hankalin duniya, wata gimbiyar kasar Malaysia ta zabi hakura da dala miliyan 300 da za ta gada don auren sahibinta.

Angeline Francis, diyar attajirin dan kasuwa Khoo Kay Peng, ta yi watsi da wa'adin da mahaifinta ya dibar mata sannan ta bi zabin zuciyarta.

Budurwa ta zabi saurayinta a kan kudi
Budurwa Ta Hakura Naira Biliyan 300 Da Za Ta Gada Daga Mahaifinta Don Ta Auri Masoyinta Hoto: UGC
Asali: UGC

Angeline Francis ta hadu da Jedidiah Francis a jami'ar Oxford. Ma'auratan sun fada tarkon son juna sannan suka yanke shawarar yin aure, duk da rashin amincewar mahaifin Angeline.

Kara karanta wannan

Uwar Bari ta Jawo Shugaba Tinubu Ya Fara Shirin Dawo da Tallafin Man Fetur

Khoo Kay Peng, wanda ya kasance daya daga cikin masu kudin Malaysia kuma masu fada aji, ya bukaci diyarsa da ta sanar da hakura da yancinta na gadon dukiyarsa ko ta kawo karshen soyayyarsu da Jedidiah.

DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar

Budurwa ta zabi so a kan kudi

Angeline Francis ta zabi soyayya a kan kudi sannan ta bar gadon gidansu a baya.

Ta dawo Najeriya da mijinta sannan ta fara sabuwar rayuwa.

Daga baya ta bayar da shaida a gaban kotu a lokacin da iyayenta ke shari’ar rabuwar aurensu, tana mai bayyana dadaukarwar da mahaifiyar ta yi da kwazon mahaifinta.

Labarin Angeline Francis da Jedidiah Francis ya haddasa cece-kuce a soshiyal midiya game da matsin lambar al'umma, son dukiya da ma yanayin soyayya ita kanta.

Labarin ya kuma sa aka dunga misalai da labaran soyayya da sadaukarwa, kamar na Romeo da Juliet.

Kara karanta wannan

Kisan Albanin Kuri: Iyalan Malamin Da Aka Kashe Sun Bayyana Halin Da Suke Ciki, Sun Ba Da Sako Ga Gwamnati

Labarin soyayyar Angeline Francis da Jedidiah Francis ya ketara iyakokin kasa kuma ya zaburar da mutane kan bayar da fifiko kan abubuwan da suka dace a rayuwa.

Ban taba kwanciya da namiji ba, tsohuwa yar shekaru 80 ta magantu

A wani labari na daban, mun ji cewa wata dattijuwar mata mai suna, Annostacia Mukarukaka, ta yi ikirarin cewa har yanzu ita tsarkakkiya ce a shekaru 80 duk da cewar ta taba auren wani namiji na dan lokaci.

Mukarukaka bata ji dadin kuruciyarta ba ma, domin mahaifiyarta ta rasu lokacin da take da shekaru hudu a duniya, insa ta barta a hannun kakarta.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Musa avatar

Aisha Musa (Hausa writer) Aisha Musa 'yar jarida ce wacce ta kwashe shekaru biyar tana aikin gogewa a harkar yada labarai. Ta kammala karatun ta a Jami'ar Ibrahim Badamasi Babangida (IBB Lapai) a shekarar 2014 tare da digirin farko a fannin Tarihi. Aisha Editan Hausa ce wacce ke amfani da kwarewa da kwazonta don karfafawa wasu gwiwar yin aiki tukuru don cimma nasara. Ta karbi lambar yabo na gwarzuwar shekarar 2021 a bangaren Hausa na Legit. Za ku iya aika mata sakonnin imel ta adireshinta aisha.musa@corp.legit.ng