Budurwa Ta Samu Kyautar N500k, Ta Duka Kan Gwiwoyinta Tana Godiya

Budurwa Ta Samu Kyautar N500k, Ta Duka Kan Gwiwoyinta Tana Godiya

  • Wata budurwa ƴar Najeriya mai kirki wacce ba ta da kuɗi sosai ta yanke shawarar taimakawa wani mutum da kuɗin mota na N500
  • Budurwar ta fashe da kuka lokacin da mutumin ya gaya mata ba taimako yake buƙata ba kawai ya gwada ta ne ya ga irin kirkin da take da shi
  • Kwanaki kaɗan bayan haka, mutumin ya dawo ya kawo mata wani akwati cike da takardun kuɗi domin yabawa da niyyar taimakonsa da ta yi

Wata matashiyar budurwa ta nuna matuƙar godiyarta lokacin da wani mutum ya ba ta kyautar akwati cike da takardun kuɗi.

A cikin wani bidiyo da ya gabata, mutumin ya yi basaja kamar talaka yana neman kuɗin mota. Duk da ba ta da kuɗi, budurwar ta ba shi N500.

Budurwa ta samu kyautar N500k
Budurwar ta yi kukan dadi bayan ta samu kyautar Hoto: @dexycreation
Asali: Instagram

Budurwar ta samu N500k da kuɗin magani

Kara karanta wannan

"Dole Sai Ka Kashe N17m": Matashi Ya Soke Aurensa Da Budurwarsa Saboda Ta Bukaci Sai An Yi Biki Na Kece Raini

Budurwar ta yi mamaki lokacin da ya ƙara mata kuɗi kan N500 da ta ba shi. Ta yi magana kan yadda take kashe kuɗi masu yawa wajen siyan maganin ciwon siga da yake damunta.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

A cikin wani sabon bidiyo, budurwar ta cika da farin ciki lokacin da ta ga kuɗin da mutane suka yi karo-karo suka haɗa mata ta hannun mutumin.

Ta samu N500k da ɗaukar ɗawainiyar rashin lafiyarta.

Budurwar cikin murna ta bayyana cewa:

"Ya ubangiji me na yi haka da ka nuna min wannan gatan?"

Legit.ng ta tattaro wasu daga cikin martanin da aka yi akan bidiyon.

labisi_esther ta rubuta:

"Haka ubangiji zai albarkaci wani a wannan ranar!!! Amen."

maobudtv ya rubuta:

"Maganar gaskiya wannan abun ya sosa min zuciya."

tosanamatosero4 ya rubuta:

"Taimakawa mutum ɗaya ba zai iya canja duniya ba amma zai kawo muhimmin sauyi ga rayuwar mutum ɗayan da aka taimaka.

Kara karanta wannan

Ba haka aka so ba: Mata mai tsammanin haihuwar da 1 ta haifo 4, ta yi bayani

solaolaibi_gaji ya rubuta:

"Allah ya ƙara yi maka albarka."

Matashi Ya Soke Aurensa Ana Dab Da Biki

A wani labarin kuma, wani matashi ya soke aurensa da wacce zai aura ana saura kwanaki kaɗan a ɗaura musu aure.

Matashin dai ya fasa auren ne bayan budurwar ta sa ta buƙaci sai ya kashe N17m domin haɗa musu shagalin biki na kece raini.

Asali: Legit.ng

Online view pixel