Manyan Labarai A Yau
Miyagun ƴan bindiga sun kai sabon mummunan farmaki a jihar Plateau inda suka halaka mutum biyu. Harin na zuwa ne kasa da sati ɗaya bayan sun kai wani harin.
Yan ta'addan Boko Haram sun farmaki ayarin motoci dauke da kayayyaki da fasinjoji a karamar hukumar Bama ta jihar Borno, sun kashe mutum biyar da sace mata 7.
A wani lissafin siyasa gwamnan jihar Imo ya aje mataimakinsa na yanzu a gefe guda inda ya nemo mace a matsayin abokiyar takararsa a zaɓen gwamnan da ke tafe.
Fadar gwamnatin tarayya ta yi ƙarin haske kan dalilin da ya sanya farashin man getur ba zai yi ƙasa ba ko da kuwa matatun man fetur ɗin ƙasar nan suna yin aiki.
Gwamnatin Kano karkashin jagorancin, Abba Kabir, ta soke lasisin makarantu masu zaman kansu a fadin jihar. Ta bukaci masu makarantun da su sabunta lasisinsu.
Kungiyar gwamnonin arewa ta mika ta'aziyya tare da jajanta wa masarautar zazzau, gwamnatin Kaduna da daukacin al'ummar Musulmi kan rushewar Masallacin Zazzau.
Fasto Boma ya bayyana cewa idan ƴan Najeriya waɗanda ba sa farin ciki da ganin Shugaba Tinubu suka ci gaba da caccakarsa, lallai zai kammala wa'adin mulkinsa.
Ofishin jakadancin Najeriya a Nijar ya fito fili ya yi magana kan batun cinnawa ginin ofishin wuta da aka ce an yi a yayin da ake zanga-zanga kan juyin mulki.
Darajar Naira ta farfaɗo akan dalar Amurka bayan ta yi mummunan faɗi a ƙadiwar canji wanda ba a taɓa ganin irin sa ba. Darajar Nairar ta ƙaru da kaso 5.2%.
Manyan Labarai A Yau
Samu kari