Manyan Labarai A Yau
An samu asarar rayukan ƴan gudun hijira mutum shida bayan wani ginin da su ke aune a ciki ya rufto musu. Ginin dai ya rufto ne bayan an yi ruwan sama mai yawa.
Masana kimiyya sun gano tana mai tsayin inci uku da ranta a kwakwalwar wata mata yar Australia mai shekaru 62. Wannan ne karo na farko da ake ganin irin haka.
Babbar kotun jihar Kano ta dakatar da hukumomin EFCC, CCB da ICPC da ga binciken shugaban hukumar karɓar ƙorafe-ƙorafen jama'a da yaƙi da cin hanci ta jihar.
Wani mutumi ya fallasa wani wajen hakar zinare a wani kauye a jihar Zamfara. Ya ce haramtacce ne kuma mallakin wani tsohon gwamna, tsohon soja kuma sanata ne.
Wasu iyali a Kano sun gamu da ibtila'i sakamakon cin kwadon garin kwaki. Sun barke da amai da gudawa inda diyarsu ta ce ga garinku sannan sauran suka galabaita.
Gwamnatin jihar Kano karkashin jagorancin Abba Kabir Yusuf, ta umurci shugabannin makarantun gaba da sakandare a jihar da su rage kudaden makaranta da kaso 50.
Hukumar FCTA ta fitar da jawabi a game da wani gini da aka ruguza a birnin tarayya na Abuja. Ainihin wanda aka mallakawa filin, wani mutumi kurum ya kama gini.
Wata mata yar kasar China mai suna Tian Dongxia da mijinta Zhao Wanlong sun dauki hankalin jama’a bayan sun haifi yara tara a cikin shekaru 13 da suka gabata.
An bayyana wanda shugaban ƙasa Bola Ahmed Tinubu yakamata ya ba muƙamin ministan matasa a gwamnatinsa. Har yanzu babu ministan matasa a gwamnatin Bola Tinubu.
Manyan Labarai A Yau
Samu kari