Atiku, Obi vs Tinubu: Babban Fasto Ya Yi Hasashen Yadda Shari'ar Zaben Shugaban Kasa Za Ta Kare

Atiku, Obi vs Tinubu: Babban Fasto Ya Yi Hasashen Yadda Shari'ar Zaben Shugaban Kasa Za Ta Kare

  • An yi hasashen Peter Obi na jam'iyyar Labour Party ya haƙura da ƙarar da ya shigar da shugaba Tinubu a kotun zaɓen shugaban ƙasa
  • Prophet David Elijah, a wani saƙo da ya fitar, ya bayyana cewa Obi zai haƙura da ƙararsa domin zaman lafiya sannan magoya bayansa za su ji haushinsa
  • Peter Obi da Atiku Abubakar na ƙalubalantar nasarar da shugaban ƙasa Bola Tinubu ya yi a zaɓe

An yi hasashen cewa Peter Obi ɗan takarar shugaban ƙasa na jam'iyyar Labour Party (LP), a zaɓen shugaban ƙasa na shekarar 2023, zai haƙura da ƙarar da ya shigar a kotun sauraron ƙararrakin zaɓen shugaban ƙasa.

Obi, wanda ya zo na uku a zaɓen, yana ƙalubalantar sakamakon zaɓen a jihohi 21, ciki har da jihohi 11 da ya lashe.

Kara karanta wannan

Hantar Tinubu Ta Kaɗa, Shugaban Jam'iyya Ya Faɗi Wanda Yake da Tabbacin Zai Samu Nasara a Kotu

Babban fasto ya hango yadda shari'ar Obi za ta kare
Babban fasto ya yi hasashen Peter Obi zai janye kara Hoto: Bola Ahmed Tinubu, Peter Obi, Atiku Abubakar
Asali: Twitter

Fasto David Kingleo Elijah na cocin Glorious Mount of Possibility Church, a wani saƙo da ya bayyana a Youtube a ranar Litinin, 28 ga watan Agusta, ya bayyana cewa ya samu wahayi Peter Obi zai haƙura da ƙarar domin a samu zaman lafiya.

Magoya bayan Peter Obi za su ji haushi

Babban faston ya bayyana cewa magoya bayan Peter Obi, waɗanda aka fi sani da "Obidients" za su ji haushi sosai lokacin da Peter Obi zai bayyana aniyarsa

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Elijah ya shawarci magoya bayan Obi da jam'iyyar da su mayar da hankali kan abin da zai faru nan gaba, saboda ka da zuciyarsu ta buga lokacin da ɗan takararsu zai janye ƙarar daga kotu.

A kalamansa:

"Na hango mutanen da zuciyarsu za ta buga saboda ɗan takararsu zai haƙura nan ba da daɗewa ba. Sannan a daidai lokacin da ɗan takarar ku ya saduda, ba ku da wani zaɓi da ya wuce ku riƙa ganin laifinsa."

Kara karanta wannan

Daga Karshe An Bayyana Abin Da Ya Haifar Da Tsadar Rayuwa a Najeriya

Peter Obi Ya Kusa Zama Shugaban Kasa, Abure

A wani labarin kuma, shugaban jam'iyyar Labour Party (LP), Julius Abure, ya bayyana cewa saura ƙiris a bayyana Peter Obi a matsayin shugaban ƙasa.

Julius Abure ya bayyana cewa ɗan takarar shugaban ƙasar na LP zai yi nasara a ƙarar da yake yin kan Shugaba Tinubu.

Asali: Legit.ng

Online view pixel