Manyan Labarai A Yau
Miyagun ƴan bindiga sun kai sabon hari a garin Funtua na jihar Katsina, inda suka salwantar da ran wani babban jami'in gwamnati mai aikin samar da tsaro.
An shiga jimamin rashin Sanata Doug Larsen mai wakiltar Dakota ta Arewa a majalisar dattawan Amurka bayan ya gamu da mummunan hatsarin jirgin sama.
Kotunan sauraron ƙararrakin zaɓen gwamnoni na cigaba da zartar da hukuncinsu kan ƙararrakin da ke gabansu. Gwamnoni takwas za su san makomarsu a Oktoba.
Rundunar ƴan sandan jihar Legas ta tabbatar da cafke mawaƙi Azeez Fashola wanda aka fi sani da Naira Marley domin amsa tambayoyi kan mutuwar tsohon yaronsa Mohbad.
Majalisar dattawan Najeriya ta yi wa dokokinta sabon garambawul inda ta haramtawa sabbin sanatoci tsayawa takarar shugaban majalisa da mataimakinsa.
Shugaban cocin Fire of Liberation Interdenominational Ministries, fasto Fabian Nna, bai tayar da matacce ba daga cikin akwati kamar yadda ake cewa.
An shiga jimami da takaici bayan wani jirgin ruwa ɗauke da fasinjoji ƴan kasuwa ya kife a cikin kogi a jihar Kebbi. Mutane da dama sun nutse a hatsarin.
Shugaban ƙasa Bola Ahmed Tinubu, ya aike da wasiƙa zuwa ga majalisar dattawan Najeriya domin neman amincewarta kan ministoci uku da ya ƙara naɗa wa.
Ɗaliban jami'ar Obafemi Awolowo da ke Ile-Ife a jihar Osun, sun kulle ƙofar shiga harabar jami'ar domin nuna adawarsu kan ƙarin kuɗin makarantar da aka yi.
Manyan Labarai A Yau
Samu kari