Yadda Matashi Ya Karbe Kwantenan Da Ya Kerawa Budurwa Bayan Sun Rabu, Bidiyon Ya Girgiza Intanet

Yadda Matashi Ya Karbe Kwantenan Da Ya Kerawa Budurwa Bayan Sun Rabu, Bidiyon Ya Girgiza Intanet

  • Wata matashiyar budurwa ta saki bidiyo mai ban tausayi bayan saurayinta ya kwace shagon kwantena da ya kera mata
  • A cewarta, saurayin nata ya kera mata shagon lokacin da soyayyarsu ke da karfi amma ya kwace abun sa bayan rabuwarsu
  • Lamarin ya haifar da zazzafan muhawara a soshiyal midiya, inda mutane da dama suka bayyana ra'ayoyinsu game da abun da saurayin ya yi

Wata matashiyar budurwa yar Najeriya, Amaka Doris, ta ba da labarin yadda tsohon saurayinta, Vene, ya karbe shagon da ya kera mata bayan rabuwarsu.

A wani bidiyo da ya yadu a soshiyal midiya, an gano wata motar daukar kaya dauke da shagon, inda aka bar Amaka cikin mamaki da kunar rai.

Saurayi ya karbe shagon kwantenansa bayan sun rabu da budurwarsa
Yadda Matashi Ya Karbe Kwantenan Da Ya Kerawa Budurwa Bayan Sun Rabu, Bidiyon Ya Girgiza Intanet Hoto: @amaka.doris/TikTok.
Asali: TikTok

Matashiya ta cika da mamaki yayin da saurayinta ya kwace shagon kwantena da ya kera mata

Kara karanta wannan

Muhammadu Buhari: Babban Sakona Ga Mutanen Najeriya a Ranar Murnar 'Yancin Kai

Ta nuna rashin yardarta cewa Vene zai iya yi mata abu haka, duk da cewar ta bayyana shawararta na rashin son ci gaba da soyayyar.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Ta ce:

"Saboda na ce bana yi kuma, tsohon saurayina ya je ya dauke shagon da ya kera mun. Sunansa Vene. Lokacin da muke soyayya komai na tafiya daidai. Ka bude mun shago, ka bude mun wannan shagon don na fara wani abu.
"Don haka bayan mun rabu sai ya je ya dauko wata mota sannan ya dauke shagon da ya kera, ya kera saboda ba gina abun ya yi ba. Kamar Vene, koda mun rabu, abun da ya kamata ka yi kenan? Kamar koda na ce bana yi kuma. Ace ka je ka dauke shagon da ka kera mun lokacin da abubuwa basa tafiya daidai."

Martanin jama'a yayin da matashi ya kwace shagon da ya kerawa budurwarsa

Kara karanta wannan

Kama Da Wane: Mutum Da Ya Sauya Siffarsa Zuwa Ta Kare Ya Shiga Tasku, Ya Ce Karnuka Ba Sa Wasa Da Shi

Wasu mutane sun yaba ma Vene kan abun da ya yi, suna masu cewa tunda Amaka ta shirya rabuwarsu, zai zamo adalci gare shi ne idan ya kwace shagon.

@SUMBODI ya ce:

"Vene godiya gareka da ka sanya mu alfahari gaba dai gaba dai."

@The_Clutch_Lawyer ya ce:

"Mista Vene, a duk inda kake, ka sani cewa yan uwanka na alfahari da kai."

@Dakson17091995 ya ce:

"Tunda kina son fara komai sabo, sabon saurayi, sabon shago mana."

@Dominion ya yi martani:

"Kina rabuwa da mai taimaka maki."

Magidanci ya yi wa budurwa alkawarin miliyan 3 don ta boye kanta ga matarsa

A wani labarin kuma, wani Alhajin birni ya shiga tasku bayan matarsa ta gano yana soyayya da wata budurwa.

Domin ganin asirinsa bai tonu ba, ya bukaci budurwar da ta nunawa matar ita yar uwarsa ce inda ya yi alkawarin bata miliyan uku da kai ta hutu waje.

Asali: Legit.ng

Online view pixel