Manyan Labarai A Yau
Gwamnan jihar Sokoto, Ahmed Aliyu ya yi magana kan nasarar da ya samu a kotun zaɓen gwamnan jihar. Gwamnan ya yaba da hukuncin kotu inda ya shawarci ƴan adawa.
Ɗan takarar ɗan majalisar dokokin jihar Delta a ƙarƙashin inuwar jam'iyyar Labour Party (LP), ya koka kan yadda ya kasa biyan basussukan da ya ci a lokacin zaɓe.
Rundunar ƴan sandan jihar Katsina ta tabbatar da cafke wasu ɗalibai ma jami'ar gwamnatin tarayya da ke Dutsinma, bisa zargin hannu a mutuwar abokin karatunsu.
An shawarci jam’iyyar NNPP da gwamnatin jihar Kano da aka tsige da su shirya ma wani zaben a nan da shekaru hudu masu zuwa maimakon barazana ga bangaren shari’a.
An samu asarar ran mutum ɗaya bayan rufin wani gini ya rufto kan wani gini da ba a kammala aikinsa ba a jami'ar jihar Taraba da ke birnin Jalingo.
Kotun sauraron ƙararrakin zaɓen gwamnan jihar Sokoto ta tabbatar da nasarar da gwamna Ahmed Aliyu na jam'iyyar APC ya samu a zaɓen gwamnan jihar.
An hana wasu kafafen yada labarai masu zaman kansu shiga harabar kotu domin yanke hukuncin karshe na kotun sauraron kararrakin zaben gwamnan jihar Sokoto.
Kotun sauraron ƙararrakin zaɓen gwamnan jihar Taraba ta tabbatar da nasarar gwamna Agbu Kefas na jam'iyyar Peoples Democratic Party (PDP) a zaɓen gwamnan jihar.
Ƙungiyar ƙwadago ƙasa (NLC) ta yi magana kan dalilin da ya hanata halartar taron da FG ta kira domin tattaunawa kan yajin aikin da ƙingiyar ke shirin yi.
Manyan Labarai A Yau
Samu kari