Kotun Zaben Gwamnan Sokoto: Jami’an Tsaro Sun Hana Yan Jarida Shiga Harabar Kotu

Kotun Zaben Gwamnan Sokoto: Jami’an Tsaro Sun Hana Yan Jarida Shiga Harabar Kotu

  • An hana yan jarida na kafafen yada labarai masu zaman kansu shiga harabar kotun sauraron kararrakin zaben gwamnan jihar Sokoto
  • An tattaro cewa yan jarida daga kafofin watsa labarai na jiha da gwamnatin tarayya kawai aka bari suka shiga kotun
  • Shugaban Hukumar SSS ya tabbatar da hakan yayin da yake jawabi ga manema labarai

Jihar Sokoto - Rahotanni da ke zuwa sun tabbatar da cewar an hana yan jarida shiga harabar kotu yayin da za a yanke hukuncin karshe a kotun sauraron kararrakin zaben gwamnan jihar Sokoto.

Kamar yadda jaridar Punch ta rahoto, an tattaro cewa yan jarida sun isa harabar kotu da misalin karfe 7:00 na safe bayan jami'an tsaro sun bincike su.

An hana yan jarida shiga harabar kotun zaben gwamnan sokoto
Kotun Zaben Gwamnan Sokoto: Jami’an Tsaro Sun Hana Yan Jarida Shiga Harabar Kotu Hoto: Twitter
Asali: UGC

Rahoton ya ce harabar kotun ya cika makil da mutane, sannan jami'an tsaro sun sa samun damar shiga cikin kotun ya zama babban aiki.

Kara karanta wannan

An Tsaurara Matakan Tsaro Yayin Da Gwamnan APC Ke Shirin Tantance Makomarsa a Kotun Zaɓe

Shugaban hukumar tsaro na SSS ya ce yan jarida da ke aiki da kafafen yada labarai na jihar da na NAN da NTA ne kawai za a bari su shiga cikin kotun, rahoton Daily Post.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

PDP na fatan samun nasara, tana kalubalantar APC

A halin da ake ciki, ana sa ran kotun zaben za ta yanke hukuncinta na karshe a yau don mai kara kuma dan takarar jam'iyyar Peoples Democratic Party (PDP), Saidu Umar da Gwamna Ahmad Aliyu (wanda ake kara) kuma dan takarar jam'iyyar All Progressives Congress (APC) a zaben gwamnan na ranar 18 ga watan Maris su san makomarsu.

Dan takarar PDP, Umar yana kalubalantar nasarar Aliyu, wanda hukumar zabe mai zaman kanta (INEC) ta ayyana a matsayin wanda ya lashe zaben bayan kammala zabe da tattara sakamako.

Kara karanta wannan

Gwamnan Kaduna: "Babu Wani Rudani a Hukuncin da Kotu Ta Yanke" Gaskiya Ta Bayyana

Baturen zabe na jihar, Bichi Amaya’u, wanda ya sanar da sakamakon zaben a Sokoto, ya ce Aliyu ya samu kuri'u 453,661 wajen kayar da babban abokin hamayyarsa kuma dan takarar PDP, Umar wanda ya samu kuri'u 404,632.

Babu rudani a hukuncin kotun Kaduna - Uba Sani

A wani labarin, gwamnan jihar Kaduna kuma dan takarar jam'iyyar All Progressives Congress (APC) a zaben ranar 18 ga watan Maris, Uba Sani ya ce babu wani rudani a hukuncin kotun zabe na ranar Alhamis, wacce ta kori karar jam'iyyar PDP da Isah Ashiru kan nasararsa.

Sani ya bayyana hakan ne yayin hira da Channels TV a shirin Politics Today a ranar Alhamis, 28 ga watan Satumba.

Asali: Legit.ng

Online view pixel