Manyan Labarai A Yau
Musa Dattijo, daya cikin alkalan da ke kotun kolin Najeriya zai yi murabus daga alkalanci a ranar Juma'a 27 ga watan Oktoban 2023 kamar yadda kotun kolin ta sanar.
Nyesom Wike, ministan babban birnin tarayya Abuja, ya yi martani a kan zargin da ake yi cewa ya bai wa Isra’ila goyon bayan Najeriya a kan Falasdinu.
Tsohon gwamnan jihar Kano, Sanata Rabiu Musa Kwankwaso, ya yi magana kan sabon shirin ba almajirai mahaddata Al-Qur'ani tallafin yin karatun zamani a jihar Kano.
Ƴan ta'addan Boko Haram ɗauke da makamai sun kai farmaki kan gidan jami'an hukumar kwastam a jihar Yobe. Ƴan ta'addan sun halaka jami'i ɗaya a yayin harin.
Tsohon hadimin tsohon shugaban ƙasa, Goodluck Jonathan, Reno Omokri ya buƙaci Shugaba Bola Tinubu ya binciki tsohon shugaban ƙasa Muhammadu Buhari.
Babban faston da ya kafa cocin Jehovah's Eye Salvation Ministry, fasto Godwin Ikuru ya yi hasashen wanda zai lashe zaɓen gwamnan jihar Kogi da ke tafe.
Wani mummunan hatsarin mota ya yi sanadiyyar salwantar da rayukan wasu matafiya mutum bakwai a jihar Osun. Matafiyan sun mutu ne bayan motarsu ta fada rami.
Tsohon mai magana da yawun da tsohon shugaban ƙasa Goodluck Jonathan, Reno Omokri, ya yi tsokaci kan yadda tsohon Shugaba Buhari ya lalata ƙasar nan.
Bayan dogon lokaci tana tsare a hannun ƴan bindigan da suka yi garkuwa da ita, wata ƴar bautar ƙasa ta samu ƴancinta daga hannun miyagu a jihar Zamfara.
Manyan Labarai A Yau
Samu kari