Zaben Gwamnoni: Dalilai 4 da Za Su Iya Sanyawa APC Ta Yi Rashin Nasara a Kogi

Zaben Gwamnoni: Dalilai 4 da Za Su Iya Sanyawa APC Ta Yi Rashin Nasara a Kogi

Lokoja, jihar Kogi - Zaɓen gwamnan jihar Kogi na ranar Asabar, 11 ga watan Nuwamba, 2023. Za a iya cewa shi ne zaɓe mai zuwa da aka fi magana a kansa.

A cewar hukumar zaɓe mai zaman kanta ta ƙasa (INEC), za a fafata zaɓen na gwamnan Kogi tare da na jihohin Imo da Bayelsa.

Jam'iyyar APC ka iya rasa jihar Kogi
Gwamna Yahaya Bello tare da dan takarar APC, Alhaji Usman Ododo Hoto: Alhaji Ahmed Usman Ododo
Asali: Facebook

A ranar 27 ga watan Janairu, 2024 ake sa ran gwamnan Kogi mai ci Yahaya Bello, zai bar mulki a karo na biyu.

Zaɓen Kogi: Yadda za a samu wanda ya yi nasara

Dole ne ɗan takarar da ya yi nasara ya samu mafi yawan ƙuri'u da aƙalla kaso 25% na ƙuri'un a kaso biyu bisa uku na ƙananan hukumomin jihar.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Kara karanta wannan

Kwankwaso Ya Bayyana Sabon Shirin Taimakon Almajirai a Jihar Kano

Jihar Kogi tana da ƙananan hukumomi 21. INEC za ta sanar da sakamakon a cibiyar tattara sakamakon zaɓe ta jihar.

A cikin wannan rahoto, Legit.ng ta rubuta dalilan da za su sanya jam'iyyar APC mai mulki ta iya yin rashin nasara a jihar Kogi.

1) Zargin mulki ta hanyar kafa wakili

Wasu ƴan adawa sun yi amanna cewa gwamna Bello, na neman wa’adi na uku ne ta hanyar kafa wakili.

Bello yana goyon bayan ɗan takarar jam’iyyar APC, Alhaji Ahmed Usman Ododo, domin ya gaje shi.

Sai dai, masu adawa da Ododo sun yi amanna cewa gwamna mai ci yana ƙoƙarin cigaba da zama a kan karagar mulki ta hanyar Ododo.

2) Adawa daga masu neman takarar gwamna a jam'iyyar APC

Ododo, wanda tsohon babban mai binciken kuɗi ne na ƙananan hukumomi a jihar Kogi, ya samu tagomashi kasancewar shi kaɗai ne ɗan takara daga yankin Kogi ta tsakiya.

Kara karanta wannan

Zaben Kogi: Babban Malamin Addini Ya Yi Magana Kan Dan Takarar Da Allah Ya Zaba

Ya kuma samu goyon bayan gwamna Bello da jam’iyyarsa (APC), wacce ita ce jam'iyyar da ke mulkin Nijeriya.

Sai dai, yana fuskantar adawa daga wasu ƴaƴan jam'iyyarsa da suka sha kaye a zaben fidda gwani.

3) Ɗan takarar APC ba daga yanki mafi yawan ƙuri'u ya fito ba

Ɗan takarar jam'iyyar Social Democratic Party (SDP), Muritala Yakubu Ajaka ba Ododo na APC ba, ya fito ne daga yankin da ya fi yawan masu kaɗa ƙuri'a da yawan jama'a, yankin Kogi ta Gabas.

Kogi ta gabas (Masarautar Igala) ita ce inda Ajaka yafi ƙarfi, wanda wasu ƴan Kogi suke yi wa kallon na ɗaya daga cikin waɗanda ake ganin za su yi nasara.

4) Ƙarfin PDP a Kogi

Ba za a iya cewa babbar jam'iyyar adawa ta PDP ba ta da ƙarfin ƙwace mulki daga hannun jam'iyyar APC ba.

Tun bayan dawowar mulkin dimokuraɗiyya a 1999, jam'iyyar PDP ta yi mulki a Kogi sau huɗu, yayin da jam'iyyar APC ta jagoranci gwamnatoci biyu a jere (Gwamna Bello).

Kara karanta wannan

Gwamnan Jihar Arewa Ya Fara Binciken Sarakunan Gargajiya Masu Taimakawa Yan Bindiga a Jiharsa

Ɗan takarar PDP shine Dino Melaye, tsohon ɗan majalisar wakilai, kuma tsohon ɗan majalisar dattawa, kuma tsohon kakakin yaƙin neman zaɓen Atiku Abubakar.

"Ododo Ne Zabin Allah", Fasto Ikuru

A wani labarin kuma, wani babban fasto ya yi hasashen wanda zai yi nasara a zaɓen gwamnan jihar Kogi da ke tafe.

Fasto Godwin Ikuru na cocin Jehovah's Eye Salvation Ministry ya yi nuni da cewa ya hango nasara a tattare da Ahmed Usman Ododo, ɗan takarar gwamnan jam'iyyar APC.

Asali: Legit.ng

Online view pixel