Jita-Jitan Rusau Ya Kare Yayin da Wike Ya Bayyana Tanadin Da Ya Yi Wa Babban Masallacin Abuja

Jita-Jitan Rusau Ya Kare Yayin da Wike Ya Bayyana Tanadin Da Ya Yi Wa Babban Masallacin Abuja

  • Nyesom Wike, ministan babban birnin tarayya, ya yi alkawarin kammala aikin gyaran masallacin kasa da ake yi a Abuja, a wata ganawa da ya yi da kwamitin kula da masallacin
  • Ministan ya bayyana muhimmancin tallafa wa kula da manyan gine-ginen kasa ba tare da la’akari da addini ba
  • Shugaban kwamitin kula da Masallacin na kasa ya yaba ma ministan bisa jajircewarsa wajen gudanar da wannan aiki tare da bayyana mahimmancin ginin

FCT, Abuja - Nyesom Wike, ministan babban birnin tarayya, ya bayar da tabbacin cewa gwamnatinsa za ta kammala aikin gyaran masallacin kasa da ake yi a Abuja.

Ministan ya dauki wannan alkawarin ne yayin da tawagar kwamitin babban masallacin na Abuja karkashin jagorancin shugabanta, Mai martaba Alhaji Yahaya Abubakar, Etsu Nupe ta kai masa ziyara ofishinsa.

Kara karanta wannan

Yakin Hamas: Ministan Abuja Wike Ya Bayyana Dalilinsa Na Ganawa Da Jakadan Isra’ila a Najeriya

Wike ya yi alkawarin kammala gyaran masallacin Abuja
Jita-Jitan Rusau Ya Kare Yayin da Wike Ya Bayyana Tanadin Da Ya Yi Wa Babban Masallacin Abuja Hoto: @OfficialFCTA
Asali: Twitter

Wata sanarwa daga daraktan labaran ofishin ministan, Anthony Ogunleye, ta nuna cewa Wike ya ce hukumar FCTA za ta ci gaba da ba babban masallacin kasar goyon baya don tabbatar da kare wannan babban gini na kasar.

“Babu wata gwamnati da za ta yi kasa a gwiwa don ba da goyon baya wajen kula da wani abin tarihi na kasa, imma na Musulunci, ko na Kiristanci. Dukkanmu, muna cikin iko; kullum muna cewa Allah ya taimakemu. Idan muka ce Allah Ya taimake mu, yaya batun wadannan cibiyoyin bautar wannan Allah da kuke kira don ya taimake ku. Idan wannan cibiyar ibada ba ta nan, ta yaya za ku fara cewa Allah Ya taimake mu?” Inji shi.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Ya bukaci shugabannin addini da kada su fada tuggun wasu yan siyasa da ke kokarin amfani da addini a matsayin makami don samun karfi a siyasa da haifar da rashin jituwa a tsakanin al’umma.

Kara karanta wannan

Mista Ibu: Tsohon Shugaban Majalisar Dattawa Bukola Saraki Ya Dauki Nauyin Asibitin Jarumin Da Ke Jinya

Shugaban masalcin Abuja ya yi martani

A martaninsa, Etsu Nupe, Alhaji Yahaya Abubakar ya yaba ma ministan bisa jajircewar da ya yi wajen gudanar da ayyukansa, sannan kuma ya yi addu’ar Allah ya kara masa jagora, hikima, da kuma ci gaba da koshin lafiya wajen gudanar da harkokin babban birnin kasar nan.

Bugu da kari, ya shaida wa ministan cewa tsohon shugaban kasa Olusegun Obasanjo ne ya samar da babban masallacin Abuja a matsayin abin tarihi na kasa, wanda hakan ya sa aka yi kokarin tara kudade domin gyara shi.

A baya dai an yi ta rade-radin cewa ministan na shirin rusa wani bangare na masallacin kasar.

Wike ya magantu kan zargin goyon bayan Isra’ila

A wani labarin, mun ji cewa Nyesom Wike, ministan babban birnin tarayya, ya karyata goyon bayan Isra'ila a kan Falasdinu a yakin da ke gudana a yankin.

Wike ya yi magana ne yayin ganawarsa da kwamitin babban masallacin kasa na Abuja karkashin jagorancin Etsu Nupe, Alhaji Abubakar Yahaya.

Asali: Legit.ng

Online view pixel