“Ba’a Yin Haka”: Wike Ya Magantu Kan Zargin Goyon Bayan Isra’ila

“Ba’a Yin Haka”: Wike Ya Magantu Kan Zargin Goyon Bayan Isra’ila

  • Ministan babban birnin tarayya, Nyesom Wike ya karyata koyon bayan Isra'ila a kan Falasdinawa a yakin da ke gudana tsakaninsu
  • Tsohon gwamnan na jihar Ribas ya yi karin haske cewa ba shi da hurumin yanke hukunci kan alakar diflomasiyyar Najeriya da wasu kasashe
  • Wike ya kuma bayyana dalilin da yasa ya gana da jakadan Isra'ila a Najeriya, Michael Freeman

FCT, Abuja - Nyesom Wike, ministan babban birnin tarayya, ya karyata goyon bayan Isra'ila a kan Falasdinu a yakin da ke gudana a yankin.

Wike ya yi magana ne yayin ganawarsa da kwamitin babban masallacin kasa na Abuja karkashin jagorancin Etsu Nupe, Alhaji Abubakar Yahaya.

Wike ya ce baya goyon bayan Isra'ila a kan Falasdinu a yakin da ke gudana a yankin
“Ba’a Yin Haka”: Wike Ya Magantu Kan Zargin Koyon Bayan Isra’ila Hoto: @officialABAT, @OfficialFCTA
Asali: Twitter

Tsohon gwamnan na jihar Ribas ya kuma yi bayanin cewa a masayinsa na minista, kundin tsarin mulki bata ba shi karfin ikon yanke hukunci kan alakar diflomasiyyar Najeriya da sauran kasashe ba, wannan ikon na hannun Shugaban kasa Bola Tinubu ne.

Kara karanta wannan

Daga Karshe Ministan Birnin Tarayya Wike Ya Bayyana Tanadin Da Ya Yi Wa Masallacin Abuja

Jaridar Vanguard ta nakalto ministan yana cewa:

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

“Ba zan iya kayyade dangantaka tsakanin wata kasa da wata kasa ba. Don haka, yana da wahala wani ya ce ina yin wannan, ina yin wancan."

Dalilin da ya sa na gana da jakadan Isra'ila a Najeriya - Wike

A ranar Talata, 3 ga watan Oktoba, jakadan Isra'ila a Najeriya, Michael Freeman, ya ziyarci ministan Abuja, kwanaki kadan kafin harin da Hamas ta kai Isra’ila da kuma ci gaban ramuwar gayya daga Yahudawa, wanda ya yi sanadin rasa dubban rayuka daga bangarorin biyu.

Sai dai kuma, ziyarar da Freeman ya kai wa Wike ya haddasa cece-kuce inda wasu suka zargi ministan da bai wa Isra'ila goyon bayan Najeriya.

Da yake karyata zargin, Wike ya ce ya gana da jakadan Isra'ila ne daga cikin shirinsa na bunkasa tsaron abinci a babban birnin tarayya.

Kara karanta wannan

Wike: Tashin Hankali Yayin da Tsohon Kakakin APC Ya Bukaci Tinubu Da Ya Kama Sheikh Gumi

Ya kara da cewar taron don nemawa manoman babban birnin tarayya hadin gwiwa a bangaren noma ne.

“A nan Abuja galibinsu suna da gonakin al’adu, sai muka ce ku duba, muradinmu ne mu taimaki duk mai son zuba jari a Abuja, musamman a fannin noma, domin a dauki mutanenmu aiki da kuma samun karin kudaden shiga. Bai da wata alaka da abun da ya shafi wata kasa. Ba haka ake yi ba," in ji Wike.

Tsohon kakakin APC ya nemi a kama Sheikh Gumi kan Wike

A wani labarin, Legit Hausa ta rahoto cewa Yekini Nabena, tsohon mataimakin sakataren labaran jam'iyyar APC na kasa, ya yi kira ga shugaban kasa Bola Tinubu da ya kama Sheikh Ahmad Gumi, shahararren malamin Musulunci mazaunin Kaduna.

Jigon na APC ya yi kira ga shugaban kasar da hukumomin tsaro a kasar da su kama malamin musuluncin kan furucin da ya yi kwanan nan a kan Nyesom Wike, ministan babban birnin tarayya.

Asali: Legit.ng

Online view pixel