Yan Ta'addan Boko Haram Sun Kai Hari Gidan Kwastam a Jihar Yobe

Yan Ta'addan Boko Haram Sun Kai Hari Gidan Kwastam a Jihar Yobe

  • Ƴan ta'addan Boko Haram ɗauke da makamai sun kai farmaki a gidan jami'an kwastam dake garin Geidam a jihar Yobe
  • Miyagun ƴan ta'addan sun kai farmakin ne da daren ranar Asabar, 21 ga watan Oktoba inda suka halaka jami'i ɗaya
  • Al'ummar garin na Geidam sun nuna damuwarsu kan yadda mayaƙan Boko Haram ke cin karensu babu babbaka a yankin

Jihar Yobe - Wasu da ake kyautata zaton mayaƙan Boko Haram ne sun kai hari a gidan jami'an kwastam da ke garin Geidam a ƙaramar hukumar Geidam ta jihar Yobe.

Ƴan ta'addan a yayin harin sun halaka wani jami'in kwastam mai suna Usman Gombe.

Mayakan Boko Haram sun halaka jami'in kwastam
Yan ta'addan Boko Haram sun kai farmaki a Yobe Hoto: Channelstv.com
Asali: UGC

Yadda harin ya auku

Jaridar Daily Trust ta tattaro cewa ƴan ta'addan sun kai farmakin ne a gidan kwastam da ke kan titin Maine Soroa a cikin wasu motoci ƙirar Golf Volkswagen da Land Rover da misalin karfe 10 na daren ranar Asabar, 21 ga watan Oktoban, inda suka fara harbe-harbe.

Kara karanta wannan

Harin Fashi a Bankuna: An Kashe DPO da Wasu 'Yan Sanda Uku a Jihar Arewa, Sabbin Bayanai Sun Fito

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Sun kai farmakin ne lokacin da suka tabbatar jami'an kwastam ɗin sun koma gida. Cikin firgita saboda ruwan harsasai, jami'an suka yi ta tururuwa domin tsira da rayukansu, wasu kuma suka tsere ta kofar shiga, yayin da wasu kuma suka tsallaka ta katanga.

Wata majiyar tsaro ta bayyana cewa:

"Sai dai, abin takaicin shi ne, an harbi ɗaya daga cikin jami'an mai suna Usman Gombe a lokacin da yake ƙoƙarin hawa katangar."

Ya ce maharan sun kuma ƙona motar sintiri ta kwastam, janareta, da wani ɓangare na ginin gidan kwastam ɗin.

"Wannan ne karo na biyu da mayakan Boko Haram ke kashe jami’an kwastam. A watan da ya gabata mahara sun yi awon gaba da wani jami'insu mai suna Babalola, da ƙaramin jami’insa, inda daga bisani maharan suka halakasu." A cewarsa.

Hare-haren Boko Haram na ƙaruwa a Geidam

Kara karanta wannan

Mutane Sun Yi Takansu Yayin da 'Yan Fashi Suka Farmaki Bankuna 2, Jami'an Tsaro Sun Mutu

Mazauna garin sun bayyana cewa ayyukan ƴan Boko Haram a wajen Geidam sun ƙaru a cikin ƴan kwanakin nan.

Wani ɗan kasuwa ya bayyana cewa:

"Suna karɓar haraji daga manoma da makiyaya masu tazarar kilomita kaɗan daga garin kuma ba wanda ke yin komai."
"A maimakon haka, jami'an tsaro sun sanya shingayen binciken ababen hawa 17 cikin garin inda kuma suke karɓar kuɗaɗen haraji a hannun ƴan kasuwar da ke shigo da kayayyaki ta hanyar. Muna cikin tsaka mai wuya a wannan garin."

Mayakan Boko Haram Sun Halaka Mutum 4

A wani labarin kuma, mayaƙan Boko Haram sun halaka mutum huɗu a wani sabon hari da suka kai a jihar Borno.

Ƴan ta'addan sun halaka mutanen ne a wani ayarin motocin da suka haɗa da ƴan sakai na CJTF da sojoji waɗanda ke raka fasinjoji a kan hanyar Gwoza Limankara.

Asali: Legit.ng

Online view pixel