Manyan Labarai A Yau
Ministan kwadago da samar da ayyukan yi, Simon Lalong ya karbi takardar shaidar cin zabe a matsayin Sanata mai wakiltar Filato ta Kudu a majalisar dokokin tarayya.
Gwamnatin jihar Zamfara ta musanta rahotannin da ake yada wa cewa Gwamna Dauda Lawal ya kashe N400m kan tafiye-tafiye zuwa kasashen waje cikin wata shida a ofis.
Wata mummunar gobara ta tashi cikin tsakar dare a wata fitacciyar kasuwa da ke birnin Ilorin babban birnin jihar Kwara. Gobarar ta laƙume shaguna masu yawa.
Alkalin Alkalin Najeriya (CJN) Olukayode Ariwoola, ya yi shagube ga Atiku da Peter Obi yayin da ya bayyana inda za a iya daukaka kara bayan hukuncin kotun koli.
Kotun daukaka kara da ke Abuja za ta yanke hukunci kan zaben gwamnan jihar Nasarawa da ake takaddama a kai. Ku biyo mu kai tsaye don jin yadda ake ciki.
Abdullahi Adamu, Tanko Al-Makura, da sauran su sun isa kotun daukaka kara yayin da za a yanke hukunci kan zaben Nasarawa mai cike da takaddama a ranar Alhamis.
Ƙungiyoyin kwadago sun bayyana cewa za su bijirewa matakin gwamnatin tarayya na rage kudin da aka ware domin karin albashi ga ma'aikatan gwamnatin tarayya.
Kotun daukaka kara da ke zamanta a birnin tarayya Abuja, za ta raba gardama kan shari'ar zaben gwamnan jihar Nasarawa bayan kotun zabe ta tsige gwamna Abdullahi.
Dakarun sojoji sun samu nasarar cafke wasu miyagun mutane masu ba yan bindiga bayanai da siyo musu kayayyaki domin gudanar da ayyukansu a jihar Kaduna.
Manyan Labarai A Yau
Samu kari