A karo Na 5, Abba Ya Sake Tura Daliban Kano Indiya Don Yin Karatun Digiri Na Biyu Kyauta

A karo Na 5, Abba Ya Sake Tura Daliban Kano Indiya Don Yin Karatun Digiri Na Biyu Kyauta

  • Gwamnan jihar Kano, Abba Kabir Yusuf ya sake tura karin dalibai 50 kasar Indiya domin su karo karatu
  • Daliban sune rukuni na biyar cikin mutum 1,100 da gwamnatin Kano ta dauki nauyin tura su waje su yi digiri na biyu
  • Kwamishinan ilimi na jihar, Dr Yusuf Kofarmata, ya bayyana cewa daliban za su yi karatu a bangarori daban-daban a manyan jami'o'i takwas na kasar

Aisha Musa ta shafe tsawon shekaru tana kawo labaran Hausa a bangaren siyasa, tsegumi da al’amuran yau da kullum

Jihar Kano - Gwamnatin jihar Kano karkashin jagorancin Abba Kabir Yusuf ta sake tura karin dalibai 50 cikin 1,100 da ta tallafin karatu zuwa kasar Indiya domin yin digiri na biyu.

Wadannan sune rukuni na biyar a jerin daliban da gwamnatin jihar ta aika kasar waje domin karo ilimi, jaridar Daily Trust ta rahoto.

Kara karanta wannan

Mulki ya zo ƙarshe: Gwamna Bello ya ɗauki mataki, ya rufe dukkan asusun Gwamnati jiharsa

Abba ya sake tura daliban Kano Indiya
A karo na 5, Abba ya sake tura daliban Kano Indiya don yin karatun digiri na biyu kyauta Hoto: @Kyusufabba.
Asali: Twitter

Wadanda suka ci gajiyar shirin sun bar filin jirgin sama na Malam Aminu Kano zuwa Lagas a jirgin Max Air da misalin karfe 7:30 na safiyar Juma'a, daga nan jirgin Air Peace ya kwashe su zuwa Indiya da karfe 2:00 na rana.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Daliban za su yi karatu a manyan jami'o'in Indiya

Da yake magana jim kadan bayan tashinsu, kwamishinan ilimi, Dr Yusuf Kofarmata wanda ya shaida lokacin tashin daliban tare da sauran jami'an gwamnati ya ce:

"Idan wadanda suka amfana suka isa Indiya, za a kwashe su zuwa makarantun jami'o'insu daban-daban da suka hada da Sharda, Symbiosis, Mewar, Sri Sai, Swarnnim da Kalinga don fara digirinsu na biyu a bangarori daban-daban."

Dr Kofarmata ya bayyana cewa daliban sun kammala da digiri mafi daraja wadanda aka zabe su bayan an duba kokarinsu.

Ya kara da cewar za su yi karatu a bangarori daban-daban don cike gibi na karancin ma'aikata a jihar da ma kasar baki daya.

Kara karanta wannan

Kano: Yayin da CTC ta tabbatar da nasarar Abba Kabir, NNPP ta fadi hanyar warware matsalar

"Jimillar dalibai 550 ne a rukunin farko wadanda za su je manyan jami'o'i takwasa don karatu a bangarori da ake ji da su a duniya don cike gibin da ake samu a jihar da ma kasa baki daya.
"Ana kuma sa ran daliban za su samu gogewa, kwarewa da ilimi da nufin sake fasalin kasuwancin jihar da kuma gano wasu hanyoyin da za su iya bunkasa zamantakewa da tattalin arziki."

Kwamishinan ya kuma bayyana cewa bayanan da gwamnatin jihar ta samu shine cewa wadanda suka ci gajiyar shirin sun riga sun fara karatunsu a bangarori daban-daban, rahoton Nigerian Tribune.

Ya kuma kara da cewar 30 daga cikin daliban sun riga sun samu aiki a makarantar da suke saboda kwazonsu kafin yaye su.

An budewa daliban Najeriya wata dama

A wani labarin, mun ji cewa dalibai daga Najeriya da wasu kasashe 14 sun samu damar neman tallafin karatu daga gidauniyar GREAT gabanin zangon karatu na shekarar 2024-25.

Tallafin zai ba daliban Najeriya da sauran kasashen damar samun Euro 10,000 don biyan kudin makaranta a shirye-shiryen karatu na matakin PGD a jami'o'in Birtaniya.

Asali: Legit.ng

Online view pixel