Yanzu: Tinubu Ya Shiga Ganawar Sirri da Dattawan Ondo Kan Rikicin Akeredolu da Aiyedatiwa

Yanzu: Tinubu Ya Shiga Ganawar Sirri da Dattawan Ondo Kan Rikicin Akeredolu da Aiyedatiwa

  • Shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu ya tsoma baki a rikicin Gwamna Rotimi Akeredolu,da mataimakinsa, Lucky Aiyedatiwa
  • A yanzu haka Tinubu na ganawar sirri da wasu masu ruwa da tsaki daga jihar Ondo yayin da suke neman mafita mai dorewa kan rikicin
  • Sanata Jimoh Ibrahim da sauran masu ruwa da tsaki na APC sun hallara a taron da ke gudana a fadar shugaban kasa

Aisha Musa ta shafe tsawon shekaru tana kawo labaran Hausa a bangaren siyasa, tsegumi da al’amuran yau da kullum

Fadar shugaban kasa, Abuja - Ana gab da samun maslaha dangane da rikicin da fe faruwa tsakanin gwamnan jihar Ondo, Rotimi Akeredolu, da mataimakinsa, Lucky Aiyedatiwa.

A yanzu haka Shugaban kasa Bola Tinubu na cikin wata ganawa da wasu shugabannin siyasa na jihar a fadar shugaban kasa da ke Abuja.

Kara karanta wannan

Shugaba Tinubu ya shiga tsakani yayin da yan majalisa suka fara shirin tsige gwamnan APC

Tinubu na ganawa da jiga-jigan jihar Ondo
Yanzu: Tinubu Ya Shiga Ganawar Sirri da Dattawan Ondo Kan Rikicin Akeredolu da Aiyedatiwa Hoto: Rotimi Akeredolu/Asiwaju Bola Ahmed Tinubu
Asali: Facebook

Kamar yadda jaridar The Nation ta rahoto, Sanata mai wakiltar Ondo ta Kudu, Sanata Jimoh Ibrahim da sauran masu ruwa da tsaki na jam'iyyar APC sun hallara a taron.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Sai dai kuma, babu tabbacin ko Gwamna Akeredolu ko mataimakonsa za su halarci taron.

Tinubu ya tsoma baki a rikicin siyasar Ondo

Da farko, Legit Hausa ta rahoto cewa Shugaban kasa Tinubu ya tsoma baki a gabar da ke tsakanin Akeredolu da Aiyedatiwa.

Wata majiya ta ce Shugaban kasa Tinubu ya gayyaci mambobin majalisar Ondo zuwa Abuja, babban birnin tarayyar Najeriya.

A makon jiya ne manyan dattawa da sarakunan gargajiya suka roki Tinubu da ya shiga tsakani a rikicin siyasar Ondo don kaucewa barkewar rikici. An tattaro cewa majalisar dokokin jihar ta rabu gida biyu inda yan majalisa 11 ke goyon bayan Aiyedatiwa a yanzu haka.

Kara karanta wannan

Shari’ar Gwamna: Cikin Yarbawa ya tsure yayin da zanga-zanga ya barke a Kano

Yan majalisar Ondo za su yi zama

A wani labarin kuma, mun ji cewa mambobin majalisar jihar Ondo sun shirya zama yau Jumu'a, 24 ga watan Nuwamba, 2023 domin tattauna sarƙaƙiyar siyasar jihar.

An tattaro daga majiya mai tushe cewa ƴan majalisar dokokin zasu fi maida hankali ne kan ɓangaren masu zartarwa na gwamnatin jihar Ondo karkashin gwamna Rotimi Akeredolu.

Bayanai sun nuna akwai yiwuwar ƴan majalisar zasu jingine gwamnan gefe guda, su ayyana mataimakin gwamna, Lucky Aiyedatiwa, a matsayin muƙaddashin gwamna.

Asali: Legit.ng

Online view pixel