Manyan Labarai A Yau
Aikin ceto da dakarun sojoji karkashin jagorancin Manjo Janar Godwin Mutkut suka yi a jihar Sokoto ya yi sanadiyar ceto mutum 31 da aka yi garkuwa da su.
Nyesom Wike, ministan babban birnin tarayya, ya sanar da sabon shirinsa na sauya tsarin sufuri a Abuja yayin da ya bukaci yan adaidaita da su fara tattara kayansu.
Gwamnan jihar Katsina, Malam Dikko Umaru Radda ya amince da fitar N977m domin biyan jarabawar NECO na shekarar 2023 ga daliban jihar har mutum 48,385.
Gwamnatin jihar Osun ta fitar da rahoton yadda aka tafiyar da kasafin kudin jihar na watanni uku tsakanin Yuli da Satumba. Gwamna Adeleke ya kashe N6bn a lokacin.
Ministan babban birnin tarayya Abuja, Nyesom Wike, ya bayyana yadda ya tara N110bn cikin watanni uku da ya kwashe a kan kujerar ministan birnin tarayya Abuja.
Wasu matan aure a birnin tarayya Abuja sun fada hannun miyagun yan bindiga dauke da makamai bayan sun kai musu farmaki suna tsaka da gudanar da aikin gona.
Hedikwatar rundunar yan sandan jihar Adamawa ta fuskanci hari da sanyin safoyar ranar Laraba, 22 ga watan Nuwamban 2023. Yan sanda na gudanar da bincike.
Majalisar dattawa a ƙarƙashin jagorancin Sanata Godswill Akpabio ta amince da naɗin Dakta Chukwuemeka Agbasi a matsayin manajan darakta na hukumar FERMA.
Kotun ɗaukaka ƙara ta saki takardun hukuncin da ta yanke kan shari'ar zaɓen gwamnan jihar Kano, wanda ya tsige Gwamna Abba Kabir Yusuf na jam'iyyar NNPP.
Manyan Labarai A Yau
Samu kari