Kotun Daukaka Kara Ta Yanke Hukunci Kan Zaben Gwamna Sule Na Nasarawa

Kotun Daukaka Kara Ta Yanke Hukunci Kan Zaben Gwamna Sule Na Nasarawa

  • Kotun daukaka kara da ke zama a Abuja ta tabbatar da zaben Gwamna Abdullagi Sule na jam'iyyar All Progressives Congress (APC) a matsayin zababben gwamnan jihar Nasarawa
  • Kotun daukaka karar a hukuncinta na ranar Alhamis, ta ce kotun zaben jihar ta yi kuskure wajen ayyana dan takarar PDP David Ombugadu, a matsayin wanda ya lashe zaben
  • Idan har Ombugadu bai kalubalancin hukuncin kotun daukaka karar ba a Kotun Koli, toh Sule ne zai jagoranci al'ummar Nasarawa har zuwa shekarar 2027

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Aisha Musa ta shafe tsawon shekaru tana kawo labaran Hausa a bangaren siyasa, tsegumi da al’amuran yau da kullum

Lafia, jihar Nasarawa - Kotun daukaka kara da ke zamanta a Abuja, ta tabbatar da zaben Gwamna Abdullahi Sule na jihar Nasarawa a ranar Alhamis, 23 ga watan Nuwamba.

Kara karanta wannan

Bayan shari'ar Nasarawa, kotu ta sake yanke hukunci kan shari'ar zaben gwamnan APC, ta ba da dalili

Kotun daukaka karar ta jingine hukuncin kotun sauraron kararrakin zabe wanda ya tsige gwamnan daga kan kujerarsa, jaridar The Cable ta rahoto.

Kotu ta tabbatar da zaben Abdullahi Sule a matsayin gwamnan jihar Nasarawa
Yanzu Yanzu: Kotun Daukaka Kara Ta Yanke Hukunci Kan Zaben Gwamna Sule Na Nasarawa Hoto: Gov. Abdullahi A. Sule Mandate
Asali: Twitter

Wannan ci gaban zai zama mummunan labari ga jam'iyyar Peoples Democratic Party (PDP) da dan takararta, David Ombugadu.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Da suke zartar da hukunci, alkalan kotun guda uku karkashin jagorancin mai shari'a Uchechukwu Onyemenam, sun amince da cewa kotun zaben ta yi kuskure wajen yanke hukuncin cewa Sule bai samu rinjayen kuri’un da aka kada a zaben ba, rahoton Channels Tv.

Bugu da kari, kotun daukaka karar ta ce an hana Gwamna Sule damar jin ta bakinsa.

Manyan jiga-jigan APC sun isa Kotu

Da farko Legit Hausa ta rahoto cewa Abdullahi Adamu, tsohon shugaban jam'iyyar APC na kasa da tsohon gwamnan jihar Nasarawa, Tanko Al-Makura, sun hallara a kotun daukaka kara yayin da za a yanke hukunci kan rikicin zaben gwamnan jihar.

Kara karanta wannan

Zaben Gwamnan Kano: Kotun Koli za ta warware rudanin da aka samu a Kotun Daukaka Kara, NNPP

Baya ga Adamu da Al-Makura, Labaran Maku, tsohon ministan labarai, da Silas Ali Agara, mataimakin gwamnan jihar Nasarawa mai ci duk sun hallara a kotun daukaka karar, gabannin yanke hukunci kan zaben gwamnan jihar.

Falana ya magantu kan zaben Kano

A wani labarin kuma, babban lauyan Najeriya kuma lauya mai kare hakkin dan adam, Femi Falana, ya sake tsoma baki a hukuncin kotun daukaka kara da ya kai ga tsige gwamnan jihar Kano, Abba Kabir Yusuf.

A wata hira da aka yi da shi a baya-bayan nan, Falana ya yi adawa da tunanin da jama'a ke yi na cewa an tsige Gwamna Yusuf, yana mai cewa kotun daukaka kara da ke zama a Abuja ta tabbatar da zaben Yusuf tare da amanna da duk abun da gwamnan ya nema.

Asali: Legit.ng

Online view pixel