Ku bar ganin Ganduje haka; raina kama ne kaga gayya - Jigo a PDP ya ankarar da Kwankwaso

Ku bar ganin Ganduje haka; raina kama ne kaga gayya - Jigo a PDP ya ankarar da Kwankwaso

  • Tarin basirar shugaban APC na kasa, Abdullahi Ganduje a siyasa yana gwara kawuna kuma ya ja hankalin jigon PDP, Reno Omokri
  • Jigon na PDP ya garzaya shafinsa na soshiyal midiya a ranar Alhamis, don jinjinawa Ganduje da dabarunsa kan yadda yake tafiyar da siyasar Najeriya
  • Omokri ya bayyana cewa Ganduje da yana da baiwa irin ta Obasanjo da Tinubu

Aisha Musa ta shafe tsawon shekaru tana kawo labaran Hausa a bangaren siyasa, tsegumi da al’amuran yau da kullum

Reno Omokri, tsohon hadimin tsohon shugaban kasa Goodluck Jonathan, ya bayyana wasu boyayyun halayen Abdullahi Ganduje, shugaban jam’iyyar APC na kasa.

Reno Omkori ya yi shagube ga Kwankwaso
“Ana Yi Wa Ganduje Kallon Wawa Amma Yana Da Tarin Basira”: Jigon PDP Ya Yi Shagube Ga Kwankwaso Hoto: Reno Omokri, Dr. Abdullahi Umar Ganduje OFR, Rabiu Kwankwaso
Asali: Facebook

Omokri ya jinjinawa dabarun siyasar Ganduje, ya caccaki Kwankwaso

A wasu jerin wallafa da ya yi a shafinsa na X (wanda aka fi sani da Twitter a baya), jigon na jam'iyyar PDP ya yi shagube ga jagoran jam'iyyar NNPP, Rabiu Kwankwaso, wanda basa ga maciji da Ganduje.

Kara karanta wannan

APC ta yi watsi da takardar CTC da ke tabbatar da Abba a matsayin gwamnan Kano: "Kuskure ne"

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Ku tuna cewa a ranar Laraba, 22 ga watan Nuwamba, kotun daukaka kara ta kara jaddada cewa ta tsige yaron Kwankwaso a siyasa kuma gwamnan jihar Kano, Abba Kabir Yusuf.

Kotun daukaka karar ta bayyana cewa abun da ya faru a kwafin takardar CTC tuntuben alkalami ne wanda ba zai sauya hukuncin kotun game da zaben Kano ba, rahoton Channels TV.

A cikin wallafar da ya yi a ranar Alhamis, 23 ga watan Nuwamba, Omokri ya nanata cewa Ganduje na da baiwa irin ta tsohon shugaban kasa Olusegun Obasanjo da Bola Ahmed Tinubu.

Omokri ya kuma bayyana cewa Ganduje, tsohon gwamnan jihar Kano bai da hayaniya kamar yadda ake tsammani, maimakon haka yana da dabara duk da ana yi masa kallon gaula, yana da tarin basira.

Jigon na PDP ya rubuta:

Kara karanta wannan

Kujera za ta haddasa sabuwar rigima tsakanin Wike da gwamnoni a Jam’iyyar PDP

"Ganduje yana da baiwa irin ta Obasanjo da Tinubu: Yana da siffar gaulaye amma yana da kaifin basira. Yana kuma da saurin ji, bai da saurin fushi, kuma yana da jinkirin magana da daukar mataki. Kuma sakamakon haka, yana da dabara, yayin da wasu da dama, musamman wadanda ke raina shi, basu da tabbass. Kuma ya fahimci tsari mafi girma a siyasa. Babu aboki ko makiyi na din-din-din. Kawai ra'ayi ne na din-din-din. Kuma fahimtar wannan tsari ne ke ba shi damar aiki da mutanen da yake so don cimma muradin da yake so."

Reno ya magantu kan tsige Abba

A wani labarin, Reno Omokri, ya yi tsokaci kan hukuncin Kotun Daukaka Kara da ta tabbatar da tsige Gwamna Abba Kabir Yusuf na jihar Kano.

Omokri ya ce tsige Abba Gida Gida ya tabbatar da tazarcen shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu a 2027.

Asali: Legit.ng

Online view pixel