Manyan Labarai A Yau
Shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu ya amince da nadin sabbin sakatarorin dindindin guda takwas a ma’aikatar tarayya da ke Abuja, a ranar Juma’a, 24 ga watan Nuwamba.
Gwamnatin jihar Kano karkashin jagorancin Abba Kabir Yusuf ta sake tura karin dalibai 50 cikin 1,100 da ta dauki nauyinsu zuwa kasar Indiya domin yin digiri na biyu.
Ministan babban birnin tarayya, Nyesom Ezenwo Wike, ya bayyana cewar ba zai yi takara da shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu ba a babban zaben Najeriya mai zuwa a 2027.
A halin yanzu dai shugaba Bola Tinubu yana ganawa da jiga-jigan siyasar Ondo kan rikicin da ke tsakanin Gwamna Rotimi Akeredolu da mataimakinsa Lucky Aiyedatiwa.
Shugabannin jam'iyyar All Progressives Congress (APC), na jihar Rivers, sun bayyana matsayarsu kan sauke su daga mukamansu da kwamitin NWC ya yi.
Kotun daukaka kara ta tabbatar da zaben gwamna Abdullahi Sule na jihar Nasarawa. Kotun daukaka kara ta yi watsi da hukuncin da kotun zabe ta yanke.
Reno Omokri, tsohon hadimin tsohon shugaban kasa, ya bayyana ra’ayinsa game da bajintar siyasar shugaban jam’iyyar APC na kasa, Abdullahi Ganduje.
Ministan kwadago da samar da ayyukan yi, Simon Lalong ya karbi takardar shaidar cin zabe a matsayin Sanata mai wakiltar Filato ta Kudu a majalisar dokokin tarayya.
Gwamnatin jihar Zamfara ta musanta rahotannin da ake yada wa cewa Gwamna Dauda Lawal ya kashe N400m kan tafiye-tafiye zuwa kasashen waje cikin wata shida a ofis.
Manyan Labarai A Yau
Samu kari