Manyan Labarai A Yau
An samu asarar rayuka mutanen da ba su ji ba, ba su gani ba yayin da wasu miyagun ƴan bindiga, suka kai mummunan farmaki kan wasu ƙauyuka a jihar Taraba.
Kotun daukaka kara da ke zamanta a birnin Legas ta tabbatar da nasarar gwamnan jihar Akwa Ibom, Fasto Umo Eno na jam'iyyar Peoples Democratic Party (PDP).
Kotun daukaka kara da ke zamanta a birnin tarayya Abuja ta bayyana iyakar da INEC za ta iya kai wa wajen kare kanta a shari'ar zabe a hukuncin da ta yanke.
Rundunar ƴan sandan jihar Kano ta haramta aiwatar da zanga-zangar da magoya bayan jam'iyyun APC da NNPP suka shirya a jihar kan hukuncin kotun daukaka kara.
Ministan birnin tarayya Abuja, Nyesom Wike, ya caccaki gwamnan jihar Rivers Siminalayi Fubara, kan butulcin da ya yi masa bayan ya hau kan mulkin jihar Rivers.
A ranar Juma'a, 24 ga watan Nuwamba, kotun daukaka kara da ke zamanta a Abuja, ta tabbatar da nasarar Nasir Idris a matsayin gwamnan jihar Kebbi.
Shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu ya amince da nadin sabbin sakatarorin dindindin guda takwas a ma’aikatar tarayya da ke Abuja, a ranar Juma’a, 24 ga watan Nuwamba.
Gwamnatin jihar Kano karkashin jagorancin Abba Kabir Yusuf ta sake tura karin dalibai 50 cikin 1,100 da ta dauki nauyinsu zuwa kasar Indiya domin yin digiri na biyu.
Ministan babban birnin tarayya, Nyesom Ezenwo Wike, ya bayyana cewar ba zai yi takara da shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu ba a babban zaben Najeriya mai zuwa a 2027.
Manyan Labarai A Yau
Samu kari