Kotun Daukaka Kara Ta Bayyana Ainahin Wanda Ya Lashe Zaben Gwamnan Kebbi

Kotun Daukaka Kara Ta Bayyana Ainahin Wanda Ya Lashe Zaben Gwamnan Kebbi

  • Kotun daukaka kara ta kori karar PDP da Janar Aminu Bandel, ta tabbatar da nasarar Nasir Idris a zaben gwamnan Kebbi
  • Yayin da ta yanke hukunci ranar Jumu'a, 24 ga watan Nuwamba, kotun ta warware korafe-korafe biyar da masu karar suka gabatar
  • Ta tabbatar da cewar Gwamna Nasir Idris ne ya lashe zaben na ranar 18 ga watan Maris

Aisha Musa ta shafe tsawon shekaru tana kawo labaran Hausa a bangaren siyasa, tsegumi da al’amuran yau da kullum

Jihar Kebbi - Kotun daukaka kara da ke zama a Abuja, ta tabbatar da nasarar Nasir Idris a matsayin sahihin zababben gwamnan jihar Kebbi a zaben ranar 18, ga watan Maris.

Kwamitin kotun mai mutum uku, ya bayyana a ranar Juma'a, 24 ga watan Nuwamba, cewa karar da jam'iyyar PDP da dan takararta na zaben gwamnan, Janar Aminu Bandel bai da inganci, jaridar Daily Trust ta rahoto.

Kara karanta wannan

Kotun daukaka kara ta yi hukunci kan shari'ar gwamnan PDP, ta ba da dalili

Kotun daukaka kara ta tabbatar da zaben Gwamna Nasir Idris na jihar Kebbi.
Kotun Daukaka Kara Ta Bayyana Ainahin Wanda Ya Lashe Zaben Gwamnan Kebbi Hoto: @NasiridrisKG
Asali: Twitter

Yadda kotun daukaka kara ta yi fatali da karar PDP kan zaben gwamnan Kebbi

A wani hukunci na bai daya da Mai shari’a Ndukwe Anyannwu ta yanke, kotun daukaka karar ta warware dukkan korafe-korafe biyar da aka gabatar inda nasara ya kai bangaren gwamnan yayin da PDP ta sha kaye.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Mai shari’a Anyanwu ta bayyana cewa zarge-zargen da ake yi wa Mataimakin Gwamna Abubakar Umar Tafida na kirkirar takardun bogi ba a kafa su kamar yadda doka ta tanadar ba.

Ta kuma tabbatar da cewar batun rashin bin tanadin dokar zabe na 2022, a yayin gudanar da zaben bai da tasiri saboda masu karar sun gaza tabbatar da yadda zargin ya shafi zaben.

Daga bisani mai shari’a Anyanwu ta tabbatar da hukuncin kotun sauraron kararrakin zaben gwamnan jihar Kebbi wadda a baya ta yi watsi da karar da PDP ta shigar tare da tabbatar da zaben gwamnan, rahoton Premium Times.

Kara karanta wannan

Kotun ɗaukaka ƙara ta yanke hukunci kan nasarar Gwamna Uba Sani na jihar Kaduna

Kotu ta tabbatar da zaben Uba Sani

A wani labari makamancin wannan, mun ji cewa kotun ɗaukaka ƙara mai zama a birnin tarayya Abuja ta tabbatar nasarar Gwamna Malama Uba Sani na jihar Kaduna.

Kwamitin alƙalai uku na Kotun a ranar Jumu'a sun yanke cewa ƙarar da jam'iyyar PDP da ɗan takararta, Isa Ashiru Kudan suka ɗaukaka ba ta cancanta ba kwata-kwata.

Kotun ɗaukaka ƙaran ta warware dukkan korafe-korafe biyar da masu ƙara suka gabatar kuma ta wanke Gwamna Uba Sani, kamar yadda jaridar Daily Trust ta ruwaito.

Asali: Legit.ng

Online view pixel