Manyan Labarai A Yau
Kwanaki 30 kenan gwamna Adeleke ya shafe a kasar Thailand inda ya ce ya je yin hutu, sabanin rade-raden da ake na cewa ya je ayi masa aiki a guiwa.
Shugaban riko na jam'iyyar All Progressives Congress (APC) a jihar Rivers ya soki salon mulkiin Gwamna Siiminalayi Fubara bayan shafa wata shida kan mulki.
Wani mummunan hatsarin jirgin ruwa da ya auku a jihar Adamawa ya ritsa da wasu mutum biyar. Mutum biyu sun rasa ransu bayan jirgin ruwan ya kife.
Rundunar yan sandan jihar Kano, ta tabbatar da cewa wasu daga cikin masu zanga-zangar da aka cafke a birnin Kano, an gurfanar da su a gaban kotu.
Ministan ma'adanai, Dele Alake, ya bayyana cewa manyan yan Najeriyan ke daukar nauyin hakar ma'adanai ba bisa ƙa'ida ba da ta'addanci da yan bindiga.
Wasu miyagun yan bindiga sun yi wa ayarin wasu motoci kwanton bauna a jihar Rivers. A yayin harin yan bindigan sun halaka sojoji hudu da direbobi biyu.
Wata kungiyar lauyoyi mai suna 'Concerned Citizens' ta yi alkawarin tattara lauyoyi 300 domin kare nasarar Bello Matawalle na jam'iyyar APC a kotun koli.
Iyalan mutanen da suka rasu a harin bam da sojoji suka kai kan masu Maulidi a kauyen Tudun Biri cikin karamar hukumar Igabi ta jihar Kaduna, sun kai FG kara.
Ƙungiyar yan kasuwa (TUC) ta bukaci shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu da ya gaggauta biyan dukkanin ma'aikantan gwamnatin tarayya karin albashin N35,000.
Manyan Labarai A Yau
Samu kari