Innalillahi: Wani Ibtila'i Ya Yi Sanadiyyar Rasuwar Mahaifiya da Jaririnta a Adamawa

Innalillahi: Wani Ibtila'i Ya Yi Sanadiyyar Rasuwar Mahaifiya da Jaririnta a Adamawa

  • Wani hatsarin jirgin ruwa da ya auku a ƙauyen Gamadio na ƙaramar hukumar Numan ya salwantar da rayukan mutum biyu
  • Hatsarin jirgin ruwan ya ritsa da mutum biyar waɗanda suke tsaka da tafiya a cikin rafi lokacin da jirgin ya kife
  • An samu nasarar ceto mutum uku daga cikin mutum biyar ɗin da hatsarin ya ritsa da su yayin da ba a gano gawarwakin mutum biyun ba

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi

Jihar Adamawa - Mutum biyu sun rasa rayukansu a wani hatsarin jirgin ruwa a ƙauyen Gamadio da ke ƙaramar hukumar Numan a jihar Adamawa.

An bayyana cewa mutum biyun da suka rasa ransu wata mahaifiya ce mai shayarwa da jaririnta, cewar rahoton Daily Trust.

Kara karanta wannan

Mummunan hatsari ya laƙume rayukan aƙalla mutane 10 a babban titi a Najeriya

Hatsarin jirgin ruwa ya halaka mutum biyu a Adamawa
Mutum biyu sun rasu a hatsarin jirgin ruwa a Adamawa
Asali: Twitter

Lamarin ya faru ne lokacin da wani jirgin ruwa ɗauke da mutum biyar ya kife yana cikin tafiya a rafi, rahoton TheCable ya tabbatar.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Har yanzu dai ba a gano gawarwakin mutum biyun da suka rasu ba har zuwa lokacin kammala haɗa wannan rahoto.

Shugaban ƙaramar hukumar Numan, Mista Christopher Sofore, wanda ya tabbatar da faruwar lamarin, ya ce an ceto sauran mutum uku da hatsarin ya ritsa da su.

Tawagar gwamnati ta kai ziyarar jaje

Sofore ya yi magana ne a lokacin da wata tawaga ƙarƙashin jagorancin mataimakiyar gwamnan jihar, Farfesa Kaletapwa George Farauta, ta ziyarci Numan.

Farfesa Farauta ta ƙalubalanci hukumomin da abin ya shafa da su tabbatar da samar da rigunan kwale-kwale da tabbatar da amfani da su domin rage asarar rayuka.

Ta kuma buƙaci masu ruwa da tsaki da su tabbatar da kai rahoton faruwar irin wannan lamari a kan lokaci ga ƴan sanda da sauran hukumomin da abin ya shafa.

Kara karanta wannan

Mako ɗaya bayan jefa bam a Kaduna, 'yan bindiga sun ƙara yin mummunar ɓarna kan bayin Allah

Mutum 24 Sun Rasu a Hatsarin Jirgin Ruwa

A wani labarin kuma, kun ji cewa aƙalla mutum 10 ne suka rasu a wani sabon hatsarin jirgin ruwa da ya afku a ƙaramar hukumar Shiroro ta jihar Neja.

Shugaban sashin kai agaji na hukumar bada agajin gaggawa ta jihar Neja (NSEMA), Alhaji Garba Salihu, ya ce hatsarin jirgin ruwa ya ritsa da kimanin fasinjoji 34 waɗanda suka haɗa da maza 20 da mata 14.

Asali: Legit.ng

Online view pixel