Matawalle Ya Samu Gagarumin Goyon Baya Da Ka Iya Sa Ya Lallasa Gwamna Dauda a Kotun Koli

Matawalle Ya Samu Gagarumin Goyon Baya Da Ka Iya Sa Ya Lallasa Gwamna Dauda a Kotun Koli

  • Bello Matawalle na jam'iyyar APC ya samu gagarumin tagomashi a shari'ar da yake da Gwamna Dauda Lawal na Zamfara
  • Wata ƙungiyar lauyoyi ta yi alƙawarin tattara lauyoyi 300 domin kare nasarar da ya samu a kotun ƙoli
  • Ƙungiyar ta yi nuni da cewa za ta kare ɗan takarar na APC ne domin ta yi amanna shi ne ya yi nasara a zaɓen gwamnan jihar

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi

FCT, Abuja - Ƙungiyar lauyoyi ta 'Concerned Citizens' ta yi alkawarin haɗa lauyoyi 300 domin kare nasarar Bello Mattawale, ɗan takarar gwamna na jam’iyyar APC a jihar Zamfara, a Kotun Koli, cewar rahoton Leadership.

Hakan na zuwa ne bayan alƙawarin da Gwamna Dauda Lawal da jam’iyyar PDP ya yi na neman haƙƙinsa a kotun ƙoli bayan hukuncin kotun ɗaukaka ƙara ya tilasta sake yin zaɓe a ƙananan hukumomi uku na jihar, Maradun, Birnin-Magaji da Bukkuyum.

Kara karanta wannan

Rivers: An ba INEC sabon wa'adi kan yan majalisar PDP da suka koma APC

Lauyoyi 300 za su kare Matawalle
Matawalle ya samu goyon bayan lauyoyi 300 Hoto: Bello Matawalle, Dauda Lawal
Asali: Twitter

Meyasa suke goyon bayan Matawalle?

Da suke jawabi ga manema labarai a Abuja ranar Lahadi, sun bayyana cewa matakin da suka ɗauka na haɗa kan ƙwararrun lauyoyi 300 na da nufin kare dimokuradiyyar kasar daga zargin magudin zabe da kuma masu yunkurin tsoratar da ɓangaren shari’a.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Kodinetan ƙungiyar na ƙasa, Bassey Ekemini, ya yi nuni da cewa dole ne Kotun Koli ta nuna ba ta dogara da kowa ba a ranar yanke hukunci tare da tabbatar da girmanta, domin kawo ƙarshen girman kan waɗanda ke tunanin suke da iko da Zamfara.

A kalamansa:

"Mun tattaro lauyoyi da dama jajirtattu masu son gaskiya da adalci. Sun tsaya a matsayin masu son gaskiya da neman adalci ga gwamnan mu mai jiran gado, Matawalle."

Wane kira suka yi ga Kotun Koli?

Ekemini ya buƙaci kotun ƙoli da ta yanke hukuncinta ba tare da tsoro ba bisa tsarin shari'a, domin tabbatar da hukuncin kotun ɗaukaka ƙara wanda ya tabbatar da nasarar mutanen Zamfara, rahoton Blueprint ya tabbatar.

Kara karanta wannan

Bayan shan kashi a zaben gwamnan Kogi, Dino Melaye ya bayyana babban darasin da ya koya

"Mun tsaya kan nasarar da aka ba Bello Matawalle a watan Maris na 2023 sannan mun buƙaci kotun ƙoli da kada ta tauye gaskiya. Dole ne alƙalai masu girma kada su bari barazana daga kafafen sadarwa ta yi tasiri a kansu." A cewarsa.

Ya kuma yi kira ga al’ummar jihar da su kwantar da hankalinsu, tare da nuna kwarin guiwar cewa za a yi adalci.

Gwamna Dauda Ya Magantu Kan Sake Zaɓe

A wani labarin kuma, kun ji cewa Gwamna Dauda Lawal na jihar Zamfara, ya nuna ƙwarin gwiwar yin nasara a zaɓen da kotun ɗaukaka ƙara ta yi umurnin sakewa a jihar.

Gwamna Dauda Lawal ya ce mutanen jihar sun yarda da shi a matsayin wanda zai tafiyar da harkokin jihar, cewa baya tsoron a sake zaɓe.

Asali: Legit.ng

Online view pixel