Murna Yayin da Yar Bautar Kasa Ta Gina Ajujuwa 2 a Makarantar da Dalibai Ke Zama a Kasan Bishiyoyi

Murna Yayin da Yar Bautar Kasa Ta Gina Ajujuwa 2 a Makarantar da Dalibai Ke Zama a Kasan Bishiyoyi

  • Makarantar firamare ta Gudum Hausawa da ke wajen cikin birnin Bauchi ta samu ajujuwa biyu
  • Wata ƴar bautar ƙasa Rahila Garba ce ta ƙaddamar da aikin, wacce tausayi ya sanya ta inganta yanayin karatun ɗaliban
  • Rahila ta ce ta yanke shawarar gina ajujuwan ne bisa ga mugun yanayin da ta samu makarantar a lokacin da aka tura ta yin bautar ƙasa

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi

Jihar Bauchi - Wata ƴar bautar ƙasa mai suna Rahila Garba ta kai ɗaukin gaggawa ga ɗalibai da malaman makarantar firamare ta Gudum Hausawa.

Ƴar bautar ƙasar ta sanya murmushi a fuskarsu ta hanyar gina ajujuwa biyu a makarantar da ke bayan garin Bauchi.

Kara karanta wannan

Yan bindiga sun halaka sojoji 4 a wani sabon hari, bayanai sun fito

Yar bautar kasa ta gina ajujuwa a Bauchi
Yar NYSC ta gina ajujuwa biyu a makarantar firamare a Bauchi Hoto: @TheVoiceofPHC
Asali: Twitter

Rahila ta ce ta yanke shawarar fara aikin ne saboda ɗalibai suna koyon karatu a ƙarƙashin bishiyoyi kuma suna zaune a ƙasa.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Kamar yadda jaridar The Punch ta ruwaito, ta bayyana hakan ne yayin da take jawabi a wajen ƙaddamar da aikin a ranar Talata 12 ga watan Disamba.

Meyasa ta gina ajujuwan a makarantar?

A kalamanta:

"A lokacin da aka turo ni nan domin yin bautar ƙasa, na fahimci cewa akwai buƙatar ƙarin ajujuwa sannan wajen bai yi kama da inda ɗalibai za su ji daɗin koyon karatu ba, saboda gaba ɗaya makarantar tana buƙatar yara yayin da ɗaliban suke koyon karatu a ƙarƙashin bishiyoyi."
"Wannan abun da na gani ne ya sanya na samo dabarar gina ƙarin ajujuwa.
"Duk da cewa da farko na sha wahala duba da yanayin ƙarfin aljihuna, amma na dage da son ganin wannan aikin ya yiwu."

Kara karanta wannan

Kungiyar TUC ta aike da muhimmin gargadi ga Shugaba Tinubu kan karin albashin N35,000

Kamar yadda The Guardian ta rahoto, ƴar bautar ƙasar ta yi kira ga gwamnatin jihar da masu hannu da shuni da su taimaka wajen samarwa makarantar ta N3.5m da kujeru da sauran abubuwa.

Ƴar Bautar Ƙasa Ta Cika da Murna

A wani labarin kuma, wata ƴar bautar ƙasa ta cika da murna bayan ta fasa asusun kuɗin alawus ɗin ta da ta samu.

Ƴar bautar ƙasar ta nuna tsantsar farin ciki kan yawan kudin da ta gani sannan ta nuna yadda ta kirga su da taimakon mutane bayan ta kwashe wata 12 tana tari.

Asali: Legit.ng

Online view pixel