Amurka Za Ta Dawowa Najeriya Dala Miliyan 8.9 da Aka Sace a Lokacin Gwamnatin Jonathan

Amurka Za Ta Dawowa Najeriya Dala Miliyan 8.9 da Aka Sace a Lokacin Gwamnatin Jonathan

  • Gwamnatin kasar New Jersey ta ce za ta dawowa Najeriya dala miliyan 8.9 da aka ajiye a bankin kasar a zamanin mulkin Jonathan
  • Kotun Jersey ce ta yanke wannan hukuncin bayan da babban mai shigar da kara na kasar ya nemi a kwace kudin saboda zargin rashawa
  • A shekarar 2014 ne aka ajiye kudaden a wani banki na kasar Jersey da sunan za a sayi makamai, amma aka gano an karkatar da su

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida.

Kotun Daukaka Kara ta New Jersey ta yanke hukuncin mayar da kadarorin da aka sace da aka kiyasta kudinsu ya kai fam miliyan 6.9 (dala miliyan 8.9) zuwa Najeriya.

A watan Nuwamba ne babban mai shigar da kara na kasar Jersey ya sanar da kwace kudin, inda ya ce akwai yiwuwar jami'an gwamnatin Najeriya sun boye kudin ne don karkatar da su a 2014.

Kara karanta wannan

FG ta saki sunayen kamfanonin Najeriya da suka cancanta su nemi kwangilar gwamnati a 2024

Amurka za ta dawo da kudin Najeriya
Amurka za ta dawowa Najeriya dallar miliyan 8.9 da aka sace a lokacin gwamnatin Jonathan. Hoto: @GEJonathan, Getty Images
Asali: Twitter

Rahotanni sun bayyana cewa an tura kudaden ne a matsayin kwangilar sayen makamai a gwamnatin Jonathan da nufin yaki da kungiyar Boko Haram a Najeriya.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Badakalar kwangilar makamai a zamanin Goodluck Jonathan

Leadership ta ruwaito cewa tsohon shugaban kasa Goodluck Jonathan na jam’iyyar PDP ya yi mulki tsakanin shekarar 2010 zuwa 2015.

Idan kuma za a iya tunawa, an tafka cece-kuce a kan sayan makamai a mulkin Jonathan, inda aka yi zargin mai ba shugaban kasa shawara kan harkokin tsaro (NSA), Sambo Dasuki ya karkatar da kudaden.

Daily Trust ta ruwaito an kama wani jirgin sama mallakin shugaban kungiyar CAN, Fasto Ayo Oritsejafor a kasar Afirka ta Kudu da tsabar kudi dala miliyan 10, wanda ake zargin kudin makamai ne.

An fara shirin dawo da kudaden zuwa Najeriya

Kara karanta wannan

"Kada ku tsinewa shugabanninmu": Sarkin Musulmi ya aika muhimmin sako ga yan Najeriya

Kotun da ke Jersey ta gano cewa, akasarin kudaden Najeriya da ke kasar an yi niyyar yin cinikin makamai da su, amma karshe ba a yi ba tun a tsohuwar jam’iyya mai mulki a Najeriya.

Babban Lauyan Jersey, Mark Temple KC, ya bayyana cewa akwai hadin gwiwar da ke tsakanin Jersey da Najeriya a shirin dawo da kudaden da aka sacen.

Temple ya jaddada tasiri na dokar kwace kadaroji ta 2018 a kasar da ke yaki da cin hanci da rashawa da kuma maido da kudade ga wadanda aka aikatawa laifukan.

Ana zargin miji da mata sun sace 'yar shekara 17 a Kano

A wani labarin, wata kotun Majistire ta ba da umurnin garkame wasu mata da miji a jihar Kano.

Ana zargin ma'auratan da sace wata yarinya 'yar shekara 17 mai suna Amira Isah Takai.

Asali: Legit.ng

Online view pixel