Gwamnan Arewa Ya Magantu Kan Sace Shugaban Karamar Hukuma a Jiharsa, Ya Aike Da Sako Ga Yan Bindiga

Gwamnan Arewa Ya Magantu Kan Sace Shugaban Karamar Hukuma a Jiharsa, Ya Aike Da Sako Ga Yan Bindiga

  • Gwamnan jihar Benue, Hyacinth Alia, ya yi magana kan sace shugaban ƙaramar hukumar Ukum da ƴan bindiga suka yi
  • Gwamnan ya buƙaci ƴan bindigan da su sako shugaban ƙaramar hukumar tare da mutum ukun dake tare da shi ba tare da wani sharaɗi ba
  • Ƴan bindigan dai sun yi awon gaba ne da shugaban ƙaramar hukumar lokacin da yake kan hanyar zuwa jana'iza

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi

Jihar Benue - Gwamna Hyacinth Alia na jihar Benue ya roƙi ƴan bindigan da suka sace shugaban riƙo na ƙaramar hukumar Ukum ta jihar, Gideon Haanongon da wasu mutum uku da su sake su ba tare da wani sharaɗi ba.

Alia ya yi wannan roƙo ne a ranar Asabar, a yayin bikin jana’izar Ter Katsina-Ala, Cif Fezanga Wombo, a filin wasa na Akume Atongo, ƙaramar hukumar Katsina-Ala ta jihar, cewar rahoton PM News.

Kara karanta wannan

Jigon NNPP ya fadi abu 1 da zai faru da alkalan Kotun Koli da Gwamna Abba ya yi rashin nasara

Gwamna Alia ya bukaci yan bindiga su sako shugaban karamar hukumar Ukum
Gwamna Alia ya bukaci yan bindiga su saki shugaban karamar hukumar Ukum da suka sace Hoto: Emmanuel Ter
Asali: Twitter

An yi garkuwa da Haanongon, mai tsaronsa, direba da kuma mataimakinsa da sanyin safiyar ranar Asabar, yayin da suke kan hanyarsu ta zuwa wurin bikin jana’izar marigayin basaraken gargajiyan.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Ya yi kira da a gaggauta sakin shugaban da aka yi garkuwa da shi da wadanda ke tare da shi, rahoton Premium Times ya tabbatar.

Wane kira Gwamna Alia ya yi?

Gwamnan ya ce gwamnatinsa a shirye take ta sa matasa su zama masu amfani a cikin al’umma, idan suka daina aikata miyagun ayyuka.

Ya yi Allah wadai da yawaitar kashe-kashe da garkuwa da mutane da ƴan bindiga ke yi a yankin, ya kuma yi gargaɗin cewa gwamnatinsa ba za ta lamunci irin waɗannan munanan ayyuka ba.

Alia ya yi kira ga masu riƙe da muƙamai da tsofaffin ƴan majalisa da kuma wasu fitattun ƴaƴan Sankara da su kira taron gaggawa domin samar da mafita mai ɗorewa kan matsalar tsaro a yankin.

Kara karanta wannan

Hankula sun tashi bayan yan bindiga sun halaka 4 daga cikin mutum 10 da suka sace a Abuja

Ya kuma ba da tabbacin cewa shawarwarin da suka bayar idan aka miƙa masa za a aiwatar da su nan take.

Gwamnan ya kuma buƙaci shugabannin gargajiya na yankin da su hada kai don samar da mafita mai dorewa a kan ƙalubalen da ke addabar yankin, inda ya ce gwamnatinsa ta kuduri aniyar ganin cewa zaman lafiya a jihar.

Atiku Ya Yi Martani Kan Kisan Nabeebah

A wani labarin kuma, kun ji cewa tsohon mataimakin shugaban ƙasa, Atiku Abubakar, ya yi martani kisan da ƴan bindiga suka yi wa Nabeehah Al-Kadriyar.

Atiku ya nuna alhininsa kan kisan da ƴan bindigan suka yi mata bayan sun sace ta tare da ƴan uwanta su shida.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng

Online view pixel