Manyan Labarai A Yau
Jigo a jam'iyyar PDP, Segun Showunmi, ya bayyana hanya mafi kyau da za a yi amfani da ita domin kayar da shugaban kasa Bola Tinubu ba tare da yin hadaka ba.
Dan takarar gwamnan jam'iyyar PDP a jihar Nasarawa, David Ombugadu, ya yi kira ga magoya bayansa da su kwantar da hankulansu kan hukuncin da Kotun Koli ta yanke.
Allah ya yi wa mai martaba Sarkin Sankera, Abu King Shuluwa rasuwa a asibitin tarayya da ke Makurdi, jihar Benue. Sarki Shuluwa ya rasu yana da shekaru 79 a duniya.
Wasu yan bindiga da ake zaton masu garkuwa da mutane ne sun bude wuta a babban titin Abuja inda suka yi awon gaba da wani mutum a hanyarsa na zuwa gida.
Jam'iyyar PDP reshen jihar Ogun ta taya gwamnan jihar Dapo Abiodun na jam'iyyar APC, murnar nasarar da ya samu a Kotun Koli kan zaben gwamnan jihar.
Olu Agunloye, ministan lantarki da karafa a karkashin gwamnatin tsohon shugaban kasa Olusegun Obasanjo ya shaki iskar yanci daga kurkukun Kuje,an tabbatar da hakan.
Gwamnan jihar Nasarawa, Abdullahi Sule, ya bayyana cewa ba zai sake neman wani mukamin siyasa ba bayan ya kammala wa'adinsa na biyu a mulkin jihar.
Shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu ya amince da sake nada Dakta Bayero Farah a matsayin shugaban hukumar Koyar Da Fasahar Sufuri ta Najeriya (NITT).
Gwamna Abba Kabir Yusuf na jihar Kano tsige wasu daraktocin KIRS guda takwas daga mukamansu, tare da umurtansu da su mika ragamar ayyuka ha mataimakansu.
Manyan Labarai A Yau
Samu kari