An Sako Tsohon Ministan Obasanjo Daga Gidan Yarin Kuje, An Bayyana Dalili

An Sako Tsohon Ministan Obasanjo Daga Gidan Yarin Kuje, An Bayyana Dalili

  • Rahotanni sun tabbatar da cewar an sako tsohon ministan lantarki da karafa, Olu Agunloye, daga gidan yarin Kuje
  • Hakan na zuwa ne bayan ya cike dukkan sharuddan da aka gindaya masa domin samun yanci daga gidan gyara halin na Abuja
  • Kakakin giyan gyaran halin Kuje ne ya tabbatar da ci gaban ga manema labarai a yammacin ranar Juma'a

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Aisha Musa ta shafe tsawon shekaru tana kawo labaran Hausa a bangaren siyasa, tsegumi da al’amuran yau da kullum

Tsohon ministan lantarki da karafa, Olu Agunloye ya shaki iskar yanci daga gidan yari na Kuje.

Jaridar Punch ta rahoto a ranar Juma'a, 19 ga watan Janairu cewa an sako Agunloye daga gidan gyara halin Kuje bayan ya cika sharuddan bayar da belinsa.

An sako tsohon minista daga kurkukun Kuje
An Sako Tsohon Minista Daga Gidan Yarin Kuje, An Bayyana Dalili Hoto: Olu Agunloye
Asali: Twitter

Mai magana da yawun gidan gyaran hali na birnin Abuja, Adamu Aduza ne ya tabbatarwa da ci gaban a yammacin ranar Juma'a, rahoton TheCable.

Kara karanta wannan

"Abun kunya ne": Shugaban EFCC ya fallasa masu bincike da ke karbar na goro, ya bada sabon umurni

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Duza ya ce:

''Zan iya tabbatar muku da cewa Agunloye ya shaki iskar yanci daga gidan yarin Kuje, biyo bayan cika sharudan beli da aka gindaya masa, an sake shi da yammacin nan da misalin karfe 5:00."

An garkame ministan Obasanjo a gidan yarin Kuje

Hukumar EFCC ce dai ta gurfanar da Agunloye a gaban kotu, bisa zarginsa da karkatar da wasu kudin aikin samar da tasha wuta ta Mambila, tun a zamanin tsohon shugaban kasa Obasanjo.

Agunloye dai ana zarginsa da badakala guda bakwai, wadanda suke da alaqa da aikin wutar ta Mambila.

Babbar kotun Abuja dake Apo ce dai ta bayar da belin tsohon ministan akan kuɗi Naira miliyan 50, da karin wasu sharuddan.

EFCC ta kama tsohon minista kan damfara

A wani labarin, mun ji a baya cewa hukumar yaki da cin hanci da rashawa ta cafke tsohon ministan kasuwanci da masana’antu, Charles Chukwuemeka Ugwuh.

Kara karanta wannan

"Taku ta ƙare" An kama ƙasurgumin mai garkuwa da mutane da ya addabi mutanen Abuja

Hukumar EFCC ta kama tsohon ministan ne bisa zarginsa da hada baki da k]ma damfarar rancen kudi kimanin Naira biliyan 3.6.

Hakan na ƙunshe ne a wata sanarwa da mai magana da yawun hukumar yaƙi da cin hanci EFCC, Dele Oyewale, ya fitar kuma hukumar ta wallafa a X watau Twitter.

Asali: Legit.ng

Online view pixel