Hukuncin Kotun Koli: Dan Takarar PDP Ya Aike da Sako Mai Muhimmanci Bayan Rigima Ta Barke a Arewa

Hukuncin Kotun Koli: Dan Takarar PDP Ya Aike da Sako Mai Muhimmanci Bayan Rigima Ta Barke a Arewa

  • Ɗan takarar gwamnan jam’iyyar PDP a jihar Nasarawa, David Ombugadu, ya yi kira ga magoga bayansa da su kwantar da hankulansu
  • Wannan dai na zuwa ne bayan tashe-tashen hankula a jihar biyo bayan sanarwar hukuncin da Kotun Ƙoli ta yanke
  • Ombugadu ya godewa magoya bayansa bisa jajircewar da suka yi kan ƙoƙarin da ya yi na karɓar ragamar mulki a jihar

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi

Lafia, Nasarawa - David Ombugadu, ɗan takarar gwamnan jam’iyyar PDP a jihar Nasarawa, ya roƙi a kwantar da hankula sakamakon tashin hankalin da ya ɓarke kan hukuncin da Kotun Ƙoli ta yanke a ranar Juma’a, 19 ga watan Janairu.

A wata sanarwa da ya aikewa majiyar Legit.ng Ombugadu ya bayyana godiyarsa ga magoya bayansa da abokan hulɗarsa.

Kara karanta wannan

Bayan nasara a Kotun Koli, gwamnan APC ya bayyana makomar siyasarsa bayan gama mulki

Ombugadu ya yi kira ga magoya bayansa
Ombugadu ya kiran da a kwantar da hankula Hoto: David Ombugadu
Asali: Facebook

A kalamansa:

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

“Duk da cewa sakamakon bai kasance abin da muke fata ba, amma ƙarfinku da sadaukarwar da ku da wasu mutane da yawa suka nuna a cikin wannan lokacin, ba mu manta da su ba.
"Jajircewar da kuka yi na bin ƙa'idojin dimokuradiyya, adalci, da kuma aƙidun da muke rike da su ya kasance abin burgewa ƙwarai da gaske."

Ombugadu ya godewa magoya bayansa

Ya kuma ƙara da cewa yunƙurinsa da burinsa na samar da ingantacciyar Nassarawa bai ragu ba sannan ya buƙaci mabiyansa da su dage wajen ganin wannan yunƙurin bai mutu ba.

Ombugadu ya bayyana goyon bayan da mabiyan suka ba shi a matsayin “madogararsa” yayin da ya gode musu bisa sadaukarwar da suka yi.

Ɗan takarar na PDP ya ce:

"Har yanzu, na gode da goyon bayanku mara kakkautawa. Ƙoƙarin gama kai na ɗaiɗaikun mutane kamar ku ne ke kawo sauyi da gaske. Ina godiya da damar da aka bani na yi muku hidima, kuma ina fatan ci gaba da haɗin gwiwa don samun kyakkyawar makoma ga jihar Nasarawa."

Kara karanta wannan

Gwamnan APC ya bayyana muhimmin abu 1 da ya kamata dan takarar PDP ya yi bayan hukuncin Kotun Koli

Gwamna Sule Ya Shawarci Ombugadu

A wani labarin kuma, kun ji cewa gwamnan jihar Nasarawa, Abdullahi Sule, ya shawarci ɗan takarar gwamnan PDP a jihar, David Ombugadu.

Gwamnan ya buƙaci Ombudagu da ya jira lokacinsa ya yi domin zama gwamnan jihar.

Asali: Legit.ng

Online view pixel