Yan bindiga sun bude wuta a babban titin Abuja, sun sace wani mutum a hanyar zuwa gida da matarsa

Yan bindiga sun bude wuta a babban titin Abuja, sun sace wani mutum a hanyar zuwa gida da matarsa

  • Yan bindiga da ake zaton masu garkuwa da mutane sun bude wa wani mutum da ke cikin motarsa wuta a babban titin Abuja
  • Bayan sun yi nasarar fasa tayar motar mutumin mai suna Abdullahi Sabo, maharan sun yi awon gaba da shi
  • Sabo na a hanyarsa na zuwa gida tare da matarsa ne a lokacin da abun ya afku, kuma matar ta yi nasarar tserewa

Aisha Musa ta shafe tsawon shekaru tana kawo labaran Hausa a bangaren siyasa, tsegumi da al’amuran yau da kullum

Abuja - A yayin da ake tsaka da fama da rashin tsaro a babban birnin tarayya Abuja, yan bindiga sun yi garkuwa da wani mutum mai suna Abdullahi Sabo.

Sabo na hanyarsa na zuwa gida tare da matarsa lokacin da yan bindiga suka tare motarsa ​​a Sabon- Lugbe, titin da zai sada mutum da filin jirgin sama a babban birnin tarayyar kasar.

Kara karanta wannan

Yadda Tinubu zai kawo karshen rashin tsaro a cikin watanni 6 Inji Janarorin Soja

Yan bindiga sun bude wuta a babban titin Abuja
Yan bindiga sun bude wuta a babban titin Abuja, sun sace wani mutum a hanyar zuwa gida da matarsa Hoto: Nigeria Police Force
Asali: Facebook

Mutumin da abun ya ritsa da shi yana tuki ne a wata motarsa kirar Lexus Jeep da lamba ABC 769 TP lokacin da mummunan al'amarin ya afku.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

An tattaro cewa ya baro cikin gari ne a hanyarsa na zuwa gida lokacin da maharan da ke cikin wata motar Golf suka budewa motarsa wuta tare da fasa tayoyin Jeep din.

Yadda lamarin ya faru

Daya daga cikin makwabtan mutumin, Daramola Joseph, wanda ya zanta da jaridar Daily Trust ta wayar tarho ya tabbatar da batun sace Sabo.

Ya ce:

"Sun harbi tayoyinsa, lamarin da ya tursasawa motar tsayawa, amma kafin sun isa kusa da motar, matar mutumin ta tsere. Sai dai kuma, sun tafi da mijinta.
"Mutumin da matarsa suna hanyarsu na dawowa daga cikin gari ne sannan sun nufi kusa da hanyar rukunin gidajen Jedo lokacin da yan bindigar suka far masu."

Kara karanta wannan

Tsige yan majalisar PDP 23: Gwamnan Filato ya ziyarci Tinubu, ya yi karin bayani

Da aka tuntubi kakakin yan sandan babban birnin tarayya, SP Adeh Josephine, ta ce za ta bincika tare da yin karin bayani, rahoton Trust Radio.

Wannan ci gaban na zuwa ne kasa da awanni 48 bayan yan bindiga sun farmaki rukunin gidajen sojoji da ke Kurudu, a Abuja tare da sace wasu mazaunan wajen.

Tsaro zai inganta a Abuja - Wike

A gefe guda, mun kawo a baya cewa ministan Abuja, Nyesom Wike ya ce jami'an tsaro sun kama wasu mutane dake kaiwa yan ta'adda kwarmato da a babban birnin tarayyar kasar.

Wike ya ce wadannan mutane suna ci gaba da taimakon bata garin da bayanai a wuraren da ayyukan bata garin yayi kamari.

Asali: Legit.ng

Online view pixel