Na Hannun Daman Atiku Ya Bayyana Dalilin Ziyartar Buhari a Daura

Na Hannun Daman Atiku Ya Bayyana Dalilin Ziyartar Buhari a Daura

  • Segun Showunmi wanda shi ne tsohon kakakin kwamitin yaƙin neman zaɓen shugaban ƙasa na Atiku Abubakar a 2023, ya yi magana kan ziyartar Buhari
  • Showunmi ya bayyana cewa ya ziyarci tsohon shugaban ƙasar ne domin au tattauna kan makomar Najeriya
  • Ya yi nuni da cewa ziyarar na da muhimmanci domin ya je koyon wasu abubuwa daga wajen Buhari waɗanda suka shafi ƙasar nan

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi

Tsohon mai magana da yawun kwamitin yaƙin neman zaɓen ɗan takarar shugaban kasa na jam’iyyar PDP, Alhaji Atiku Abubakar, Segun Sowunmi, ya bayyana dalilin ziyartar tsohon shugaban ƙasa Muhammadu Buhari.

Showunmi ya bayyana cewa ziyarar da ya kai wa tsohon shugaban ƙasan a kwanakin baya, ya kai ta ne domin tattaunawa kan makomar Najeriya.

Kara karanta wannan

Bayan nasara a Kotun Koli, gwamnan APC ya bayyana makomar siyasarsa bayan gama mulki

Showunmi ya fadi dalilin ziyartar Buhari
Segun Showunmi ya yi magana kan ziyarar da ya kai wa Buhari a Daura Hoto: @SegunShowunmi
Asali: Twitter

A cewarsa, ya ziyarci tsohon shugaban ƙasar ne domin ya koyi abubuwa daga wajensa kan ƙasar nan saboda ya shafe shekara takwas yana hidimtawa Najeriya.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Showunmi dai ya sha suka bayan ya raba hotunan ziyarar da ya kai wa tsohon shugaban a shafin sa na sada zumunta.

Hakan ya zo ne kwanaki kaɗan bayan da mai magana da yawun kwamitin yaƙin neman zaɓen Atiku Abubakar, Daniel Bwala, shi ma ya ziyarci Shugaba Bola Tinubu.

Meyasa Showunmi ya ziyarci Buhari?

Da yake magana a wata hira da jaridar Punch ta Lahadi, Showunmi ya ce manufarsa ta ziyarar ita ce yin koyi da ƙwarewar Buhari, yana mai cewa, "Watakila zan zama shugaba gobe."

A kalamansa:

"Na je na ziyarce shi (Buhari) ne domin in yi wannan tattaunawa da mutum zai yi da mai gogewa kamar tsohon shugaban ƙasa Muhammadu Buhari. Na je na yi masa tambayoyin da suka dame ni a kan makomar ƙasar nan kuma na yi sa'a, na haɗu da shi, ya tarbe ni cikin farin ciki. Ya ce da ni, kai ɗana ne, za ka iya zuwa duk lokacin da kake son zuwa.

Kara karanta wannan

Bayan nasara a Kotun Koli, gwamnan APC ya aike da sako mai zafi ga dan takarar PDP

"Wani abu da ya kamata al’ummar Najeriya su fahimta shi ne, yana da sauƙi mutane su zauna su riƙa cin mutuncin shugabanninsu idan al’amura suka lalace, suna tunanin siyasa ce suke takawa. Ba na yin haka.
"A koyaushe ina tsammanin cewa dole ne a sami dalilin da ya sa abubuwa ba su tafi yadda ya kamata ba kuma wani lokacin idan na sami damar ganawa da irin waɗannan shugabannin na kan yi tambayoyi akan abin da ya faru wataƙila gobe zan iya zama shugaba.
"Zan yi koyi da wasu abubuwan da suka faru, na mutunta wasu daga cikin gudunmawar da suka bayar kuma zan iya gode musu da ƙoƙarin da suka yi domin muna magana ne game da ƙasa mai kimanin mutane miliyan 220."

Showunmi Ya Magantu Kan Haɗaka

A wani labarin kuma, kun ji cewa tsohon ɗan takarar gwamnan jihar Ogun na jam'iyyar PDP, Segun Showunmi, ya yi magana kan batun haɗakar jam'iyyun siyasa domin kawar da Tinubu a 2027.

Showunmi ya bayyana cewa PDP ba ta buƙatar yin haɗaka da wata jam'iyya kafin ta iya kawar da Tinubu a zaɓen 2027.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng

Online view pixel