A Tsinci Gawar Wata Mace a Otel Cikin Mummunan Yanayi a Yola Bayan Tafiyar Mutumin Da Suka Taho Tare

A Tsinci Gawar Wata Mace a Otel Cikin Mummunan Yanayi a Yola Bayan Tafiyar Mutumin Da Suka Taho Tare

  • Wani lamari na bakin ciki da tayar da hankali ya faru a Yola, babban birnin jihar Adamawa yayin da aka gano gawar wata mace
  • Kwamishinan yan sandan jihar Adamawa, CP Afolabi Babatola ya tabbatar da afkuwar lamarin, ya kara da cewa ya bada umurnin fara bincike nan take
  • CP Babatola ya kuma yi kira ga masu otel-otel a jihar su rika gaggawar kai wa yan sanda rahoton duk wani wanda ba su gamsu da yanayinsa ba

Yola, Jihar Adamawa - An yi wa wata mata kisar gilla a otel a Yola, babban birnin jihar Adamawa.

Afolabi Babatola, kwamishinan rundunar yan sanda ta jihar Adamawa, ya tabbatar da afkuwar abin bakin cikin, ya kuma ce ya bada umurnin a fara bincike.

Yan sanda sun fara bincike bayan gano gawar wata mata a dakin Otel a Yola
Kwamishinan yan sanda ya bada umurnin fara bincike bayan gano gawar wata mata a dakin Otel a Yola. Hoto: Rundunar Yan Sanda
Asali: Twitter

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Kara karanta wannan

Satar mutane a Abuja: "Mun kama wasu masu yiwa yan bindiga leken asiri", Wike ya yi karin bayani

CP Babatola ya bayyana kwarin gwiwa cewa za a kamo wadanda suka aikata mummunan lamarin tare da hukunta duk wanda aka samu da hannu.

Ya kuma yi kira ga masu otel-otel su rika gaggawar kai wa yan sanda rahoton duk wani wanda ba su gamsu da halayensa ba.

Mun fara bincike don gano wanda ya kashe matar a Otel, CP na Yola

Kwamishinan ya jadadda cewa kiyayye lafiya da rayyukan dukkan mazauna jihar shine abu mafi muhimmanci a garesu don haka ba za lamunci irin wannan lamarin ba, rahoton Daily Trust.

Ya ce rundunar yan sanda reshen jihar Adamawa, tare da hadin gwiwa da sauran hukumomin tsaro, sun aiki tukuru don ganin an hukunta wadanda suka aikata abin bisa tsarin doka.

Shugaban yan sandan ya yi roko ga mazauna jihar su kwantar da hankulansu, yana tabbatar musu da cewa aka kokarin tabbatar da tsaronsu.

Mummunan yanayin da aka tarar da gawar matar a Otel a Yola

Kara karanta wannan

Tsige yan majalisar PDP 23: Gwamnan Filato ya ziyarci Tinubu, ya yi karin bayani

A cewar rahotanni, wadanda ake zargin ya shigo otel din tare da wacce abin ya faru da ita, amma daga bisani ya sanar da ma'aikatan cewa zai fita ya yi wani abu ya dawo.

Sai dai, bayan an shiga dakin wanda ake zargin, ma'aikatan otel din suka tsinga gawar matar ba tare da kai ba.

An Tsinci Gawar Budurwa a Dakin Otel Bayan Sun Tafi Hutawa da Saurayi

A wani rahoton mai kama da wannan, an tsinci gawar wata mace a wani otel da ke Morogbo a unguwar Badagry a jihar Legas.

Jaridar The Punch ta ruwaito cewa lamarin ya faru ne a ranar Juma’a 31 ga watan Nuwamba.

Asali: Legit.ng

Online view pixel