Manyan Labarai A Yau
Gwamnan jihar Nasarawa, Abdullahi Sule ya yi martani kan zanga-zangar da masu adawa ke yi bayan nasarar da ya samu a Kotun Koli. Ya ce ba za ta sauya hukuncin ba.
A gurfanar da matashi mai suna Garzali Musa Obasanjo a gaban kotun shari'ar addinin musulunci dake filin hoki a jihar Kano, kan zargin cin mutunci Sheikh Triumph.
Shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu ya yi ganawar sirri da shugaban jam'iyyar APC na kasa, Dakta Abdullahi Umar Ganduje, da jiga-jigan jam'iyyar na jihar Kano.
Miyagun yan bindiga dauke da makamai da ke kai hare-haren ta'addanci sun raba mazauna kauyuka 10 na karamar hukumar Giwa ta jihar Kaduna da matsugunansu.
Majalisar Koli ta shari’ar Musulunci ta kasa ta bayyana cewa ta dawo daga rakiyar gwamnatin Shugaban kasa Bola Tinubu saboda yin watsi da muradin Musulmi.
Dakarun sojoji tare da hadin gwiwar sauran jami'an tsaro, sun samu nasarar ceto wasu mutane da yan bindiga suka sace a jihar Benue. Sun kuma fatattaki miyagun.
Rundunar yan sanda ta bayyana ikirarin cewa hukumar tsaron ta taba daukar kasurgumin dan bindiga, Bello Turji aiki a matsayin karya. ACP Adejobi ne ya karyata hakan.
Iyalan Nabeeha Al-Kadriyar sun bayyana cewa suna cikin tashin hankali yayin da suke jiran kiran yan bindigar da suka sace yaransu bayan cikar wa'adin da suka basu.
Wata kotun shari'ar musulunci ta zartar da hukunci kan wanu barawon babur da aka gurfanar da shi a gabanta a jihar Kano. Kotun ta tura shi zuwa gidan gyaran hali.
Manyan Labarai A Yau
Samu kari