Bayan Nasara a Kotun Koli, Gwamnan APC Ya Bayyana Makomar Siyasarsa Bayan Ya Gama Mulki

Bayan Nasara a Kotun Koli, Gwamnan APC Ya Bayyana Makomar Siyasarsa Bayan Ya Gama Mulki

  • Gwamnan jihar Nasarawa, Abdullahi Sule ya bayyana cewa ba zai sake neman wani muƙami ba bayan ya kammala wa'adinsa na biyu
  • Gwamnan ya bayyana hakan ne bayan Kotun Ƙoli ta tabbatar da nasararsa a matsayin gwamnan jihar
  • Sule ya yi nuni da cewa tun farko burinsa dama shi ne ya yi gwamna kawai domin baya ra'ayin wani muƙami bayan nan

Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi

Jihar Nasarawa - Gwamna Abdullahi Sule na jihar Nasarawa, ya ce ba shi da wani shiri na tsayawa takarar kowane muƙami na siyasa, bayan ya kammala wa’adinsa na biyu a matsayin gwamnan jihar.

Sule ya bayyana haka ne a lokacin da yake magana a kan nasarar da ya samu a Kotun Ƙoli yayin wata hira da gidan talabijin na Channels tv a shirinsu na 'Siyasa a yau'.

Kara karanta wannan

Hukuncin Kotun Koli: Dan takarar PDP ya aike da sako mai muhimmanci bayan rigima ta barke a Arewa

Gwamna Sule ya ce ba zai sake takara ba
Gwamna Abdullahi Sule ya ce ba zai sake neman wani mukami ba Hoto: Abdullahi Sule
Asali: Facebook

Kotun Ƙolin dai ta tabbatar da zaɓen Gwamna Sule a ranar Juma’a, 19 ga watan Janairu.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Kwamitin alƙalai biyar ƙarƙashin jagorancin mai shari’a Kudirat Kekere-Ekun ya bayyana cewa ɗaukaka ƙarar da ɗan takarar gwamna na jam’iyyar PDP, David Ombugadu ya yi ba ta da wani inganci.

Amma yayin hirar, Sule ya gaya wa David Ombugadu ya jira lokacinsa.

'Ba ni da burin neman wani muƙami', Gwamna Sule

A kalamansa:

"Na zo ne kawai don in zama gwamna. Ni ban zo na zama shugaban ƙaramar hukuma, sanata ko ɗan majalisar wakilai ba. Ba ni da wani buri kan waɗannan ofisoshin.
"Ba ni da burin zama ko da shugaban ƙasa. Ba ni da burin yin hakan. Zan iya gaya muku sarai cewa Abdullahi Sule ba zai je majalisar dattawa ba bayan ya bar mulki. Lokacin da na gama shekaru takwas na iya yin duk abin da nake so in yi.

Kara karanta wannan

Gwamnan APC ya bayyana muhimmin abu 1 da ya kamata dan takarar PDP ya yi bayan hukuncin Kotun Koli

"Ina faɗa da kwarin gwiwa cewa ba ni da niyyar tsayawa takarar kujerar Sanata. Kuna iya ajiye wannan kaset ɗin ku kunna shi wata rana."

Gwamna Uba Sani Ya Yabi Isah Ashiru

A wani labarin kuma, kun ji cewa gwamnan jihar Kaduna, Malam Uba Sani, ya yaba wa abokin takararsa na jam'iyyar PDP, Isa Ashiru Kudan.

Uba Sani ya kuma buƙacesa da ya zo su haɗa kansu domin ciyar da jihar gaba bayan Kotun Ƙoli ta tabbatar da nasararsa.

Asali: Legit.ng

Online view pixel