El-Rufai Ya Shirya Yin Fada da Gwamnatin Shugaba Tinubu, Bayanai Sun Fito

El-Rufai Ya Shirya Yin Fada da Gwamnatin Shugaba Tinubu, Bayanai Sun Fito

  • Watanni takwas bayan da majalisar dattawa ta ki amincewa da shi, rahotanni sun ce tsohon gwamnan jihar Kaduna, Nasir El-Rufai, zai fara taƙaddama da gwamnatin Bola Tinubu
  • Duk da cewa suna jam’iyya ɗaya, akwai alamun cewa El-Rufai da Shugaba Tinubu ba aminan juna ba ne
  • Bayan da aka hana shi damar zama minista a 2023, haɗe da jita-jitar da ake yaɗawa na cewa yana sha'awar shugabancin Najeriya a 2027, El-Rufai ya yanke shawarar ɗaukar mataki

Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi

FCT, Abuja - Nasir Ahmad El-Rufai, tsohon gwamnan jihar Kaduna yana shirin "yaƙi" da Shugaba Bola Tinubu a aƙalla kotuna biyu.

Kamar yadda jaridar Vanguard ta ruwaito a ranar Asabar, 6 ga watan Afrilu, za a gabatar da faɗan ne a kotunan Najeriya.

Kara karanta wannan

Hajjin bana: Daga karshe NAHCON ta bayyana adadin maniyyatan da za su sauke farali

El-Rufai zai kai Tinubu kotu
Alamu na nuna cewa akwai matsala a tsakanin El-Rufai da Tinubu Hoto: @elrufai, @DOlusegun
Asali: Twitter

El-Rufai na sa ran wanke sunansa daga zargin cewa yana da hatsarin tsaro wanda ya hana shi samun muƙamin minista.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Meyasa El-Rufai zai je kotu?

Tsohon gwamnan yana son wanke kansa ne bayan da wasu masu sharhi suka ce zai ƙalubalanci sake tsayawa takarar Shugaba Tinubu a 2027.

Rahotanni sun ce na kusa da El Rufa’i sun bayyana cewa gwamnatin Tinubu ta wulaƙanta tsohon gwamnan a bainar jama’a.

Rashin samun muƙamin na El-Rufai ya ba na kusa da shi mamaki duba da irin rawar da ya taka wajen sanya gwamnonin Arewacin Najeriya suka marawa Tinubu baya a lokacin zaɓen 2023.

Jaridar Vanguard ta ambato wani na kusa da El Rufai yana cewa:

"Kuna tunanin cewa Mallam zai bari wannan tambarin ya tsaya a kansa? Ina mai tabbatar muku da cewa zai wanke sunansa a gaban kotu."

Kara karanta wannan

Shugaba Tinubu ya naɗa matashi ɗan shekara 36 a babban muƙami, ya faɗi wasu kalamai

El-Rufai ya gana da shugabannin SDP

A wani labarin kuma, kun ji cewa Tsohon gwamnan jihar Kaduna, Malam Nasir Ahmed El-Rufa'i ya ziyarci shugabannin jam'iyyar adawa ta SDP.

Tsohon gwamnan ya kai wannan ziyarar ne yayin da ake ci gaba da raɗe-raɗin cewa yana shirin tattara ƴan komatsansa ya fice daga jam'iyyar APC mai mulki.

Asali: Legit.ng

Online view pixel