Dakarun Sojojin Sun Hallaka Tantiran 'Yan Ta'adda 3 a Jihar Arewa

Dakarun Sojojin Sun Hallaka Tantiran 'Yan Ta'adda 3 a Jihar Arewa

  • Dakarun rundunar sojojin Najeriya sun samu nasarar sheƙe ƴan ta'adda mutum uku a jihar Kaduna
  • Sojojin sun hallaka ƴan ta'addan ne bayan sun yi musu kwanton ɓauna lokacin da suke kan hanyarsu ta kai gyaran baburansu
  • Bayan tura tsagerun zuwa barzahu, jami'an tsaron sun kuma ƙwato babura da makamai daga hannun tantiran

Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi

Kidandan, jihar Kaduna - Rundunar sojojin Najeriya a ranar Asabar, 6 ga watan Afrilu, ta ce dakarunta sun kashe ƴan ta'adda a jihar Kaduna.

Kakkabe ƴan ta’addan dai ya faru ne a wani harin kwantan bauna da aka kai musu jihar Kaduna.

Sojoji sun hallaka 'yan ta'adda
Dakarun sojoji sun sheke 'yan ta'adda a Kaduna Hoto: HQ Nigerian Army
Asali: Facebook

Wata sanarwa da rundunar sojojin ta sanya a shafinta na X (wanda a baya a ka fi sani da Twitter) ta tabbatar da hakan.

Kara karanta wannan

Bayan abin da ya faru a Delta 'yan ta'adda sun sake yi wa sojoji kwanton bauna, an rasa mutum 6

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Rundunar ta bayyana cewa dakarun sojojin sun farmaki ƴan ta'addan ne bayan sun yi aiki da sahihan bayanan sirri.

Yadda aka kashe ƴan ta'addan

Ƴan ta'addan dai suna kan babura ne lokacin da suka yi kaciɓus da jami'an tsaron waɗanda suka aika su zuwa barzahu.

Wani ɓanagare na sanarwar na cewa:

"A yayin farmakin da aka kai ranar Juma’a 5 ga watan Afrilu, 2024, a kusa da ƙauyen Kidandan, ƙaramar hukumar Giwa ta jihar Kaduna, sojoji sun yi artabu da ƴan ta’adda, inda suka kashe mutum uku daga cikinsu.
"Ƴan ta’addan na kan hanya ne domin kai gyaran baburansu, waɗanda suke yin amfani da su a lokacin da suke ƙaddamar da ayyukan ta’addanci a kan al’ummar jihar Kaduna da kuma yankin Arewa maso Yamma."
"Bugu da ƙari, farmakin ya kai ga ƙwato bindiga ƙirar AK-47 guda daya, harsasan bindiga kirar AK-47, babura guda huɗu, da kuma rediyon Motorola guda ɗaya."

Kara karanta wannan

Murna yayin da 'yan sanda suka ceto mutum 100 da aka sace a Arewa, sun hallaka 'yan bindiga

Sojoji sun samu yabo

Legit Hausa ta tuntuɓi wani mazaunin yankin mai suna Abdulmalik Sani, wanda ya yaba sosai kan wannan nasarar da sojojin suka samu.

Ya bayyana cewa nasarar abin a yaba ce kuma abin farin ciki duba da yadda ƴan ta'adda suka daɗe suna addabar su a yankin.

A kalamansa:

"Wannan nasara ce mai kyau kuma muna addu'ar Allah ya ƙara wa sojojin nan ƙarfin gwiwar ci gaba da ganin bayan waɗannan miyagun mutanen."

Ya bayyana cewa a yanzu kam sai dai su ce Alhamdulillah domin al'amuran tsaro sun fara daidaita a yankin saɓanin kwanakin baya.

Sojoji sun hallaka ƴan ta'adda

A wani labarin kuma, kun ji cewa Dakarun sojojin Najeriya sun yi nasarar kashe ƴan ta’adda guda biyar a jihar Taraba.

Sojojin sun kuma daƙile yunƙurin yin garkuwa da wasu mutane a coci tare da ƙwato tarin makamai da alburusai a hannun ƴan ta'addan.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng

Online view pixel