EFCC Ta Cafke Babban Malamin Addini a Najeriya Kan Zambar N3.9m

EFCC Ta Cafke Babban Malamin Addini a Najeriya Kan Zambar N3.9m

  • Jami’an EFCC sun kama babban faston cocin CAC Freedom City Prophetic and Deliverance Ministry, Ilorin, Adeniyi Abiodun James
  • An kama babban malamin addinin ne da laifin damfarar wani mamban cocin maƙudan kuɗi har N3,980,000
  • Faston ya yi iƙirarin cewa ya samu wahayi cewa mamban cocinsa, Oluwole Babarinsa zai yi tafiya zuwa ƙasashen waje

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi

Ilorin, jihar Kwara - Jami'an hukumar EFCC sun kama babban faston cocin CAC Freedom City Prophetic and Deliverance Ministry, Ilorin, Adeniyi Abiodun James, bisa zargin damfarar wani mamban cocin kuɗi N3,980,000.

Shugaban sashen yaɗa labarai na hukumar EFCC, Dele Oyewale, ya bayyana hakan a wata sanarwa da ya fitar a ranar Asabar, 6 ga watan Afrilun 2024.

Kara karanta wannan

Emefiele: Shugaba Tinubu ya kawo ƙarshen bincike a babban banki CBN, ya ɗauki mataki

EFCC ta cafke babban fasto
Ana zargin fasto da damfarar mamban cocinsa N3.9m Hoto: @AbiodunBorisade
Asali: Twitter

Menene dalilin EFCC na cafke faston?

Oyewale ya ce wanda abin ya shafa, Oluwole Babarinsa a cikin wata takardar koke ya yi zargin cewa fasto James ya bayyana masa cewa ya samu wahayi cewa zai tafi ƙasar waje.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Kamar yadda Daily Trust ta ruwaito, Babarinsa ya ce hakan ya faru ne a lokacin wani shirin coci a shekarar 2021.

Ya ƙara da cewa faston ya tambaye shi game da ƙasar da ya fi so, sai ya amsa da "Canada".

Mai shigar da ƙarar ya ce sun amince su tattauna daga baya domin gudanar da cikakken shirin tafiyar.

A kalamansa:

"Daga baya faston ya gaya min cewa yana da wani aboki a Legas wanda zai taimaka min wajen sauƙaƙa tafiya ta zuwa Canada, amma akan Naira miliyan 1.7 da kuma Naira miliyan 2.5 domin samun tikitin jirgi da takardun tafiye-tafiye."

Kara karanta wannan

Dala ta yi muguwar faɗuwa, ta dawo ƙasa da N700 a Najeriya? Gaskiya ta bayyana

Ya kuma ƙara da ya sayar da wasu kadarorinsa da ciyo bashi domin ya samu ya tara N3,980,000 saboda tafiya Canada cikin gaggawa, inji rahoton jaridar The Punch.

Meyasa ya nemi a dawo masa da kuɗinsa

Babarinsa ya ce ya harzuƙa ne bayan ya daɗe yana jira ba tare da wani sakamako ba.

Ya ƙara da cewa hakan ne ya sanya ya fara shakku kan wahayin da faston ya samu inda ya buƙace shi da ya dawo masa da kuɗinsa.

Ya ce duk ƙoƙarin da ya yi domin ganin wanda ake zargin ya dawo masa da kuɗinsa, amma hakan ya ci tura.

Fasto ya damfari mabiyansa

A wani labarin kuma, kun ji cewa wani fasto a Amurka, Eli Regalado da matarsa, Kaitlyn, sun sayar da wani kirifto da ake kira INDXcoin ga Kiristoci a Colorado, tare da da ba su tabbacin cewa za su yi arziki.

Mutane 300 ne suka zuba jarin dala miliyan 3.2 a cikin abin da Regalado da matarsa ​​suka yi iƙirarin cewa umarni ne daga Allah.

Asali: Legit.ng

Online view pixel