Borno: Mummunar Gobara Ta Sake Tashi a Babbar Kasuwar da Ake Ji da Ita

Borno: Mummunar Gobara Ta Sake Tashi a Babbar Kasuwar da Ake Ji da Ita

  • An sake samun tashin mummunar gobara a kasuwar Gamboru da ke cikin birnin Maiduguri babban birnin jihar Borno
  • Gobarar wacce ta tashi cikin dare ba ta jawo asarar rai ba, bayan jami'an hukumar kashe gobara sun yi nasarar kashe ta
  • Kwamishinan yaɗa labarai na jihar wanda ya tabbatar da aukuwar lamarin ya ce gobarar ta tashi ne a layin ƴan katako na kasuwar

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi

Jihar Borno - An sake samun tashin gobara a kasuwar Gamboru da ke kusa da unguwar Kwastam a Maiduguri babban birnin jihar Borno.

Kwamishinan ƴada labarai da tsaron cikin gida, Alhaji Usman Tar, ya tabbatar da aukuwar gobarar, cewar rahoton jaridar PM News.

Gobara ta tashi a jihar Borno
Gobara ta tashi a kasuwar Gamboru cikin Maiduguri Hoto: @Fedfireng
Asali: Facebook

Kwamishinan ya bayyana cewa gobarar ta tashi ne a layin ƴan katako da sauran wasu sassan kasuwar.

Kara karanta wannan

'Yan bindiga sun kashe babban ɗan kasuwa a Arewa, sun ɗauke matarsa da maƙwabcinsa

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

A ranar 18 ga watan Maris, 2023 da ranar 13 ga watan Nuwamba, 2023 gobara ta tashi a kasuwar, wacce take ɗaya daga cikin manyan kasuwannin da ake da su a birnin Maiduguri.

Yaushe gobarar ta auku?

Jaridar The Punch ta ambato kwamishinan a cikin wata sanarwa, ya ce gobarar ta faru ne a ranar Laraba da misalin ƙarfe 10:00 na dare, jami’an hukumar kashe gobara ne suka yi nasarar kashe ta.

A kalamansa:

"Cikin gaggawa hukumar kashe gobara ta jihar Borno ta aika da jami'anta zuwa kasuwar, inda suka samu nasarar kashe gobarar."
"Ba a samu asarar rai ko jikkata ba a sakamakon gobarar. Kasuwar ba ta fuskantar wata barazanar tsaro daga masu aikata ɓarna."

A cewarsa, hukumar kashe gobara da hukumar bayar da agajin gaggawa ta jihar (SEMA) suna gudanar da bincike domin gano musabbabin faruwar lamarin da matakan kaucewa aukuwar hakan nan gaba.

Kara karanta wannan

Abuja: Mummunar gobara ta tashi a gidan shugaban karamar hukuma

Gobara ta tashi a jihar Kwara

A wani labarin kuma, kun ji cewa wata mummunar gobara da ta tashi ta babbake shaguna da dama a babbar kasuwar Owode da ke Offa, jihar Kwara.

Mummunar gobarar dai ta tashi ne da safiyar ranar Talata, 2 ga watan Afirilun 2024, ta jawo ƴan kasuwa sun yi asara mai tarin yawa.

Asali: Legit.ng

Online view pixel