Murna Yayin da 'Yan Sanda Suka Ceto Mutum 100 da Aka Sace a Jihar Arewa, Sun Hallaka 'Yan Bindiga

Murna Yayin da 'Yan Sanda Suka Ceto Mutum 100 da Aka Sace a Jihar Arewa, Sun Hallaka 'Yan Bindiga

  • Rundunar ƴan sandan jihar Ƙatsina ta sanar da nasarorin da ta samu a tsakanin ranakun 1 zuwa 31 ga watan Maris 2024
  • Kakakin rundunar wanda ya bayyana hakan ya ce rundunar ta sheƙe mugayen ƴan bindiga mutum biyar
  • Ya kuma sanar da cewa jami'an rundunar sun ceto mutum 100 da aka yi garkuwa da su tare da ƙwato dabbobi 658 da aka sace

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi

Jihar Katsina - Rundunar ƴan sandan jihar Katsina ta ce ta kashe mutum biyar da ake zargin ƴan bindiga ne a jihar.

Rundunar ƴan sandan ta kuma sanar da cewa ta ceto sama da mutum 100 da aka yi garkuwa da su tare da ƙwato dabbobi 658 da aka sace, cewar rahoton tashar Channels.

Kara karanta wannan

Dan majalisa ya fadi kokarin da zai yi a samu tsaro a jihar Zamfara

'Yan sanda sun hallaka 'yan bindiga
'Yan sanda sun ceto mutum 100 da aka sace a Katsina Hoto: @PoliceNG
Asali: Facebook

Wannan nasarar dai an sameta ne tsakanin ranar 1 zuwa 31 ga watan Maris na shekarar 2024.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

A cikin wannan lokacin, an kai jimillar rahotanni 51 na manyan laifuffuka kamar fashi da makami, garkuwa da mutane, kisan kai, satar shanu da dai sauransu, sannan an gurfanar da guda 30 a gaban kotu.

Waɗanne nasarori rundunar ta samu?

Jaridar Gazettengr ta ce kakakin rundunar ƴan sandan jihar, ASP Abubakar Sadiq Aliyu, ne ya bayyana hakan a wata zantawa da manema labarai ranar Juma'a.

Kakakin rundunar dai ya tattauna da manema labaran ne a hedkwatar rundunar da ke Katsina, inda ya tabbatar da cewa an cafke mutum 64 da ake zargi da aikata waɗannan laifuka.

Ya bayyana cewa, an kama jimillar mutane tara da ake zargin ƴan fashi da makami ne, mutum 11 da ake zargi da aikata laifin kisa, mutum 29 da ake zargi da aikata fyaɗe, da kuma adadin mutum 19 da ake zargi da aikata laifuka daban-daban.

Kara karanta wannan

Dakarun sojoji sun hallaka tantiran 'yan ta'adda 3 a jihar Arewa

Muhammad Auwal ya bayyana cewa Legit Hausa cewa tabbas jami'an ƴan sandan sun yi namijin ƙoƙari kan wannan nasarar da suka samu.

Ya yaba da ƙoƙarin da ƴan sandan ke yi domin ganin zaman lafiya ya dawo a jihar Katsina tare da kawo ƙarshen masu tada ƙayar baya.

Auwal ya kuma buƙaci ƴan sandan da su ƙara zage damtse domin ganin sun kawar da aikata miyagun laifuka a jihar.

Ƴan sanda sun cafke mutum 100

A wani labarin kuma, kun ji cewa rundunar ƴan sandan jihar Kano ta ce jami’anta sun kama mutane 120 da ake zargi da aikata laifuka a jihar a cikin watan Maris.

Jami'in hulɗa da jama'a na rundunar ƴan sandan jihar, Abdullahi Haruna Kiyawa, shi ne ya bayyana haka a wata sanarwa da ya wallafa a manhajar X watau Twitter.

Asali: Legit.ng

Online view pixel