Yadda Gwamnan Arewa Ya Kashe N21bn Wajen Rabon Kayan Tallafi a Jiharsa

Yadda Gwamnan Arewa Ya Kashe N21bn Wajen Rabon Kayan Tallafi a Jiharsa

  • Gwamnatin jihar Kebbi ta narkar da kuɗaɗe masu yawa wajen bayar da tallafi ga al'ummar jihar
  • Kwamishinan yaɗa labarai na jihar ya bayyana cewa gwamnatin ta kashe N21bn wajen bayar da kayayyakin tallafi
  • Kayayyakin tallafin da aka raba sun haɗa da kayan noma, kayan abinci domin inganta rayuwa al'ummar jihar

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi

Jihar Kebbi - Gwamnatin jihar Kebbi ta ce ta kashe sama da Naira biliyan 21 wajen samar da kayan tallafi ga al'ummar jihar.

Tallafin ya shafi rarraba kayan abinci, kayan amfanin gona, da kuma raba tallafin kuɗi domin inganta rayuwar mutanen jihar, cewar rahoton jaridar The Nation.

Gwamnatin Kebbi ta kashe N21bn
An raba tallafin N21bn ga al'ummar jihar Kebbi Hoto: @NasiridrisKG
Asali: Facebook

Alhaji Yakubu Ahmad-BK, kwamishinan yaɗa labarai da al’adu na jihar ya bayyana haka a lokacin da yake zantawa da manema labarai a Birnin Kebbi, babban birnin jihar a ranar Asabar, cewar rahoton Stallion Times.

Kara karanta wannan

Karin kudin wuta: Kano da sauran jihohi 12 da suka shirya inganta wuta ga al'ummarsu

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Yadda gwamnatin Kebbi ta kashe N21bn

Ya bayyana cewa gwamnati ta raba takin zamani na Naira biliyan 2.6 ga manoma kyauta domin bunƙasa noma da samar da abinci.

A kalamansa:

"Bugu da ƙari kuma, an kashe Naira biliyan 8.5 wajen siyan famfuna masu amfani da hasken rana, na’urorin canja famfo, injinan feshi don tallafa wa manoma da rage kuɗaɗen da suke kashewa.

Ahmad-BK ya ƙara da cewa gwamnatin ta sayo ɗaruruwan tireloli na hatsi na biliyoyin Naira, inda ya ce an sayo manyan motoci na abinci sama da 200 tare da rabawa jama’a kyauta a faɗin jihar domin gudanar da azumin watan Ramadan.

Kwamishinan ya ce bai ji daɗin yadda ƴan adawa suka mayar da martani kan abin da ya faru na satar kayan abinci a rumbun ajiya na gwamnati da kuma murabus ɗin babban limamin masallacin Juma’a mafi daɗewa a Birnin Kebbi.

Kara karanta wannan

Hajjin 2024: Gwamnan Arewa ya bai wa mahajjata tallafin maƙudan kuɗi bayan an yi ƙarin N1.9m

An yabi Gwamna Idris

Legit Hausa ta samu jin ta bakin wani mazaunin jihar Kebbi mai suna, Lukman Isah, wanda ya yaba kan wannan namijin ƙoƙarin da gwamnan ya yi wajen tallafawa al'ummar jihar.

Ya bayyana cewa haƙiƙa ya shaida da rabon tallafin domin ya ga waɗanda suka amfana saɓanin wanda a baya ba haka abin yake ba.

A kalamansa:

"Eh gaskiya waɗannan kuɗaɗe da mai girma Gwamna ya kashe abin a yaba ne domin mutane da dama sun amfana. Ni dai a wajen mu ban ga na tallafin famfuna masu amfani da hasken rana ba amma tabbas an raba kayan abinci."

Tallafin N3.3bn ga maniyyata

A wani labarin kuma, kun ji cewa gwamnatin jihar Kebbi ta ware maƙudan kuɗi domin tallafawa maniyya aikin hajji a jihar.

Gwamna Nasir Idris ya ware N3.34bn ga maniyyata 3,344 da ke jihar domin rage musu karin kudin da hukumar alhazai ta yi.

Asali: Legit.ng

Online view pixel