Zargin Cushe a Kasafin Kudi: Shugaban Majalisa Akpabio Ya Sake Shiga Sabuwar Matsala

Zargin Cushe a Kasafin Kudi: Shugaban Majalisa Akpabio Ya Sake Shiga Sabuwar Matsala

  • Ƙungiyar SERAP ta kai ƙarar shugaban majalisar dattawa, Sanata Godswill Akpabio, ƙara a gaban kotu
  • Ƙungiyar ta shigar da ƙarar ne saboda gazawarsa na dawo da Sanata Abdul Ningi bayan an dakatar da shi
  • Lauyoyin SERAP ne suka shigar da ƙarar a gaban babbar kotun tarayya da ke birnin tarayya Abuja

Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi

FCT, Abuja - Ƙungiyar SERAP ta maka shugaban majalisar dattawa Sanata Godswill Akpabio, ƙara a gaban kotu.

SERAP na ƙarar Akpabio ne kan rashin miƙa zargin cushen N3.7tr a kasafin kuɗi ga hukumomin yaƙi da cin hanci domin gudanar da bincike.

SERAP ta kai karar Akpabio
Kungiyar SERAP ta maka Akpabio a gaban kotu
Asali: Twitter

Meyasa aka kai ƙarar Akpabio?

Dalili na biyu na shigar da shi ƙara a gaban kotu shi ne gazawarsa wajen dawo da Sanata Abdul Ningi, wanda aka dakatar bayan ya yi fallasa kan zargin cushen.

Kara karanta wannan

Dan majalisa ya fadi kokarin da zai yi a samu tsaro a jihar Zamfara

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Lauyoyin SERAP, Kolawole Oluwadare da Adelanke Aremo ne suka shigar da ƙarar mai lamba FHC/ABJ/CS/452/2024 a ranar Juma'a, 5 ga watan Afirilu a babbar kotun tarayya da ke Abuja.

Hakan dai na ƙunshe a cikin wata sanarwa da ƙungiyar ta sanya a shafinta na X a ranar Lahadi, 7 ga watan Afirilun 2024.

Me SERAP take buƙata?

SERAP na buƙatar umurnin kotu na tilasta Akpabio miƙa batun zargin cushen N3.7tr a kasafin kuɗin ga hukumomin yaƙi da cin hanci domin bincike da tuhumar waɗanda ake zargi.

Tana buƙatar kotu ta umurci tare da tilasta Akpabio ya ɗauki matakin tabbatar da dawo da Sanata Abdul Ningi wanda aka dakatar kan zargin da ya yi na cewa an yi cushen N3.7tr a kasafin kuɗin.

SERAP ta kuma buƙaci kotun da ta umurci tare da tilasta Akpabio sanya matakan gaskiya domin tabbatar da cewa kuɗaɗen da aka ware domin ayyukan da aka sanya a kasafin kuɗin ba a wawushe su ba.

Kara karanta wannan

'Yan sanda sun cafke matasa masu yunkurin kona sansanin 'yan gudun hijira a jihar Arewa

SERAP za ta maka Tinubu kotu

A wani labarin kuma, kun ji cewa ƙungiyar SERAP ta yi barazanar daukar matakin shari'a a kan gwamnatin tarayya kan shirin kafa dokar amfani da shafukan sada zumunta.

Ƙungiyar ta ce manufar gwamnati ta saba da kundin tsarin mulkin kasar da ka'idojin kare hakkin bil'adama na kasa da ƙasa.

Asali: Legit.ng

Online view pixel