Manyan Labarai A Yau
Ministan babban birnin tarayya Abuja, Nyesom Ezenwo Wike, ya yi karin haske kan rikicin siyasar da ke tsakaninsa da gwamnan jihar Ribas, Siminalayi Fubara.
Tsohon mataimakin sakataren yada labarai na jam'iyyar APC na kasa, Yekini Nabena, ya bayyana cewa shugaban kasa Bola Tinubu sai ya shekara takwas kan mulki.
Wasu miyagun 'yan bindiga sun kai hari a dakin kwanan dalibai na jami'ar tarayya da ke Wukari a jihar Taraba. Rahotanni sun tabbatar da aukuwar lamarin.
Dakatacciyar shugabar matan jam'iyyar APC a jihar Kaduna, Maryam Suleiman, ta fito ta gayawa duniya cewa tana nan kan bakanta kan sukar Gwamna Uba Sani.
Hukumar kula da asibitoci ta jihar Kano ta dauki matakin ladabtarwa kan wasu ma'aikatan lafiya da aka samu sun cin zalin marasa lafiya a a asibitocin jihar.
Rundunar 'yan sandan jihar Bauchi ta tabbatar da cafke wani matashi bisa zarginsa da laifin hallaka yayansa. Rahotanni sun ce fada ne ya barke a tsakaninsu.
Wasu miyagun 'yan bindiga sun kutsa cikin dakin kwanan dalibai na jami'ar Calabar (UNICAL), inda suka yi awon gaba da wasu mutum uku yayin harin.
Wasu matasa sun dira kan rumubunan ajiyar gwamnati a jihar Kebbi inda suka tafka barna. Mutanen dai sun dasa wawa kan kayan abincin da aka ajiye a wurin.
Deji Adeyanju ya yi magana kan kamun ludayin ayyukan ministocin shugaban kasa, Bola Ahmed Tinubu. Lauyan ya lissafo ministocin da ya kamata a kora.
Manyan Labarai A Yau
Samu kari